Connect with us

KASASHEN WAJE

Donald Trump Ya Yi Kira Da A Maida Iran Saniyar Ware

Published

on

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke hallartar taron Kolin MDD cewa, su maida gwamnatin Iran saniyar ware muddun ta ci gaba da cin zali, yayin da ya zargi shugabannin Iran da haddasa rudani da mutuwa da kuma barna.” Trump ya ce, shugabannin Iran “basu mutunta makwabtansu ko kan iyakokinsu ko sauran kasashe. A maimakon haka shugabannin Iran suna azurta kansu da dukiyar kasar, yayin da kuma suke haddasa tashin hankali a gabas ta tsakiya da kuma wadansu yankuna dake nesa. Trump ya jadada cewa, yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar zamanin mulkin Obama na kawo karshen ayyukan nukiliyan Iran, wanda ya janye, wata garabasa ce kawai shugabannin Iran suka samu, da ya bada damar kara karfin ayyukan sojin kasar Iran da kimanin kashi arba’in cikin dari, da kuma daukar nauyin ayyukan ta’addanci da aikata ta’assa a Syria da kuma Yemen.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: