Rundunar ‘yansandan farin kaya (DSS) a Jihar Sakkwato, ta mika wasu mutane bakwai da ta ceto ga gwamnatin jihar, kasa da sa’o’i 24 da sace su.
Da yake bayyana yadda aka kubutar da wadanda lamarin ya shafa, daraktan DSS a jihar, Abdulfatah Olawuno, ya ce sun samu labarin sace mutanen da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Gundungul.
- Shugaban Kasar Suriname: Tunanin Shugaba Xi Jinping Ya Samar Da Sabuwar Hanyar Bunkasa Duniya
- PDP Ta Lashi Takobin Warware Rikicin Shugabancinta A Watan Agusta
“A yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Gundungul, jami’an DSS sun yi artabu da ‘yan bindigar.
“Tun da farko ‘yan bindigar sun kashe mutane biyu a kauyen Gundungul kafin su yi awon gaba da mutanen da aka ceto.
“Dukkanin mutanen bakwai da aka ceto DSS ta gwada lafiyarsu, kafin mika su ga gwamnatin jihar,” in ji Olawuno.
Ya kara tabbatar da shirin hukumar na tabbatar da tsaro tare da neman goyon bayan al’ummar Jihar Sakkwato.
Da yake karbar wadanda aka ceto a madadin gwamnatin jihar, sakataren gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa, ya yaba wa DSS bisa bajintar da suka yi na ceto mutanen.
Ya kuma tabbatar wa da hukumomin tsaro a jihar cewa gwamnatin jihar na ci gaba da bayar da goyon baya don tabbatar da tsaro a jihar.
“Mun yaba wa DSS kan wannan aiki kuma a matsayinmu na gwamnati mai kishin kasa, za mu ci gaba da tallafa wa ma’aikata da sauran jami’an tsaro domin su gudanar da ayyukansu,” in ji Sifawa.
Sakataren ya kuma sanar da tallafin Naira 100,000 da gwamnatin jihar ta bai wa kowane daga cikin wadanda aka ceto daga hannun ‘yan bindigar.