Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta ce jami’anta da sauran ‘yan uwanta, a ranar Litinin din da ta gabata, sun kai samame maboyar ‘yan ta’adda a jihohin Kaduna da Kano, inda suka cafke wasu mutum uku.
Wadanda ake zargin sun yi amfani da abubuwa masu fashewa kan jami’an tsaro da suka hada da sojojin Nijeriya.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyen Filato
- Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi
Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Dokta Peter Afunanya, ya bayyana cewa, a yayin farmakin da suka kai Jihar Kaduna, ‘yan ta’addan sun baza makamai masu guba a kan jami’an tsaro da ke yaki da su.
Ya ce: “Dakarun sojojin Nijeriya da na ‘yan sanda, a safiyar ranar 15 ga watan Mayu, 2023 a lokaci guda sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a sassan Kaduna da Kano.
“A yayin farmakin da suka kai jihar Kaduna, ‘yan ta’addan sun jefa wa jami’an tsaro bama-bamai.
“Daya daga cikin ‘yan ta’addan da ya sanya rigar kunar bakin wake ya tarwatsa kansa. Yayin da aka kama wasu mutane uku da ake zargi.
“Abubuwan da aka gano a wani bincike da aka yi a maboyarsu, an samu rigar din kunar bakin wake guda biyu, bindiga AK-47 daya da kuma bindigar tafi-da-gidanka guda daya.”
A halin da ake ciki kuma, a Jihar Kano, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce an kama mutane biyu a yayin da aka kwato kayayyakin da suka hada da bindiga, wayoyin hannu 11, gurneti guda biyu, AK-47 guda biyu, mota kirar Peugeot 307 daya da katin shaida mallakin wanda ake zargi da tserewa.
“Da farko dai bayanan sirri sun nuna cewa manyan ‘yan ta’adda na sake haduwa a yankin Arewa maso Yamma domin aiwatar da munanan ayyuka a yankin, musamman yadda ayyukan soji ke ci gaba da yi a yankin Arewa maso Gabas ya sanya ‘yan ta’addan tserewa zuwa shiyyar Arewa maso Yamma.
“Hukumar ta yaba wa sojojin Nijeriya da ‘yan sandan Nijeriya bisa jajircewa da goyon bayan da suka bayar wanda ya kai ga samun nasarar aikin, ci gaba da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, ba tare da wata shakka ba, wani canji ne wajen daukar matakan dakile barazanar.
“Har ila yau, Hukumar na fatan bayyana karara cewa, za ta ci gaba da hada kai da ‘yan’uwa hukumomin domin kawar da miyagun laifuka musamman a wannan lokaci na mika mulki da ma bayan mika mulki, “in ji Afunanya.