Kimanin manonan tumatir dubu uku da ke Jihar Kano, za su amfana da fasahar adana tumatir a karkashin shirin da wata kungiya mai zaman kanta, mai suna ‘Pydera Global YieldWise Nigeria’ ta kirkiro da shi.
Kungiyar ta fito da shirin ne don rage wa manoman na tumatir da ke jihar yawan asarar da suke yi, a kasuwar tumatirin din.
Aikin, wanda kuma gidauniyar Rockefeller ce ta samar da kudi don yinsa, an kirkiro da shi ne don magance asarar da manoman na tumatir suke yi a lokacin da suka dasa shi da kuma kan sauran amfanin gona da ake shuka wa a kasar nan.
Daraktan shirin Lekan Tobi ne ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da shirin a kauyen Kwanar Agalawa da ke cikin karamar hukumar Garunmalam da ke jihar ta Kano a ranar Talatar da ta wuce.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, ya ruwaito cewar, kauyen na Kwanar Agalawa, yana daya daga cikin yankunan da ake noma tumatir mai yawa a jihar.
A cewar Mista Tobi, kungiyar ta yanke shawarar kirkiro da aikin ne don shawo kan kalubalen da manoman suke fuskan ta ne a yankin.
Ya ci gaba da cewa, manoman tumatir su dubu uku da aka zabo daga cikin kungiyoyin manoma arba’in da hudu ne za su amfana da shirin, inda za a samar musu da wajen adana tumatir da kuma sarrafa shi.
Ya bayyana cewar, manoman suna da zabin samo musu sayen tumatir din su da kuma samun ingantaccen irin tumatir don samun yin noma mai riba.
Ya yi nuni da cewa, a bisa fasahar, za kuma a koyawa manoman yadda za su adana Kokumba da Albasa da Shinkafa da masara da sauransu.
Shi kuwa a nasa jawabain a wurin taron, Mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Nasiru Gawuna, ya ce gwamnatin jihar zata ci gaba da baiwa fannin aikin gona fifiko, musamman don samar da wadataccen abinci a jihar.
Mataimakin gwamnan wanda babban sakatatare a ma’aikatar aikin gona da albarkantu na jihar Aminu Garba ya wakilce shi a wurin taron mataimakin gwamnan ya kuma ya ba a kan kirkiro da shirin na YieldWise Nijeriya.
Taron ya kuma samu halartar masu noma tumatir da sauran masu ruwa da tsaki a fannin, harda wakilan da suka fito daga jihar Jigawa da Katsina da Kaduna da kuma Folato.