Ƙungiyar Matasan Arewa da ke Kudancin Nijeriya ta yi gargaɗin cewa duk wani ɗan siyasa da ya shiga rigar Jagoran Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya lashe zaɓe kuma daga bisani ya kauce wa hanyar da Kwankwason ke bi, zai gani a ƙwaryar cin tuwonsa idan Allah ya kai mu zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin ne a wani taron manema labarai na musamman da ta kira a Kano domin faɗakar da ‘yan siyasa da kuma ‘yan arewa game da muhimmancin nuna kishin yankin musamman a yanzu da aka rantsar da sabuwar gwamnati a ƙasa baki ɗaya.
Da yake ƙarin haske ga wakilinmu bayan kammala taron, shugaban ƙungiyar, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya yi nuni da cewa, akwai ‘yan siyasa da dama da suka ci alfarmar jagoran na NNPP, Sanata Kwankwaso suka samu kujerun majalisa, “amma mun san ‘yan siyasar Nijeriya suna da wata ɗabi’a, za su shiga rigar mutum su samu abin da suke so, da zarar sun samu sai su kauce. To muna kira ga waɗanda suka shiga rigar ɗan kishin mutanen arewa da babu kamarsa wajen nuna wa al’ummarmu kishi, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, suka lashe zaɓe musamman a majalisun dokoki na ƙasa da na jihohi cewa kar su ci amana su kauce wa hanyarsa. Idan suka ƙi ji, to kowa ya sani, mu talakawa da muke da ƙuri’u a hannunmu za mu yi tsayin daka wajen ganin ba su koma ba, kowa zai gani a ƙwaryar cin tuwonsa.
“Abin da ya sa muke wannan kiran a kan Kwankwaso shi ne, duk cikin ‘yan siyasar da muke da su a arewa babu wanda yake nuna kishin al’umma a fili irin Kwankwaso. Mu da muke kudu, mun shaida irin yadda yake kai-komo a duk lokacin da aka ce ga wani abu ya samu wani ɗan arewa a can. Idan ba a manta ba, a zamanin da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi yake Gwamnan Anambara, ya bayar da umarni ga kowane ɗan arewa ya yi wata shaida da za a riƙa gane shi da ita. Ba tare da wani ɓata lokaci ba, shi ma Kwankwaso ya ce kowane Ibo da ke Kano ya yi uniform da za a riƙa gane su da shi.
“Haka nan lokacin da aka tsare mutanenmu a can. ƙungiyarmu musamman a Legas ita take ruwa da tsaki wurin fitar da mutanenmu da aka tsare daga gidan yari. Kuɗin da ake cin tarar mutanenmu daga kan dubu ɗaya har zuwa dubu ɗari (100,000) duk nakan yi ƙoƙarin biya ba tare da na saurari wani mai muƙami ko wata gwamnati ba. Aƙalla yanzu tsakanin kudu da arewa muna da mambobi sama da dubu takwas. Muna iya bakin ƙoƙari wajen ganin mun kare haƙƙin arewa, shi ya sa muke ƙara jaddada kira ga duk waɗanda suka kamata cewa mu yi wa kanmu karatun ta-natsu, idan Allah ya kai mu 2027 mu haɗa kai mu tabbatar da nasarar Sanata Kwankwaso a matsayinsa na ɗan kishin al’umma da ƙasa baki ɗaya.” In ji shi.
Wakazalika, Alhaji Ya’u Ibrahim Galadanci, ya buƙaci ‘yan siyasar da ke mayar da ‘ya`yan talakawa ‘yan shaye-shaye su sani Allah yana kallonsu kuma al’umma ba za ta ƙyale ba. “Sai dai su tura ‘ya’yansu zuwa ƙasashen Turai su yi karatu a can, amma sai su haɗa `ya’yan talakawa da kayan shaye-shaye don su riƙa amfani da su ana cin mutuncin masu mutunci. To, duk wannan ya kamata al’umma ta fito ta yi maganinsu ta hanyar ƙin zaɓarsu, idan aka yi haka za a samu sauƙi sosai ko kuma a magance lamarin.” Kamar yadda ya bayyana.