Wani rahoto daga kamfanin MTN da Airtel sun nuna cewa masu amfani da waya Nijeriya suna amfani da Data aƙalla kusan 9GB kowanne wata.
Rahoton MTN ya nuna cewa matsakaicin mai amfani da data na kashe Naira ₦1,869 a kowane wata a shekarar 2023, wanda hakan ke nuna ya karu da kashi 16.3% daga ₦1,607 a shekarar 2022. Wannan dai ya yi daidai da ƙaruwar amfani da Data da kashi 27%, daga 7GB a kowane wata a shekarar 2022 zuwa 8.9GB a shekarar 2023.
- Umarnin CBN Na Cire Harajin Tsaron Intanet Ya Tayar Da Kura
- Yanzu-yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Harajin Tsaron Intanet Kan Hada-hadar Kudade
Kuɗin da kamfanin MTN ke samu ta hanyar sayen Data ya ƙaru sosai daga Naira biliyan ₦764.8b a shekarar 2022 zuwa Naira tiriliyan ₦1.07t a shekarar 2023.
Haka zalika rahoton kamfanin Airtel ya nuna kuɗin da ake kashewa a Data ga kowanne matsakaicin abokin mai amfani da Datar yana kashe ₦3,127 ($2.4) a kowanne wata, tun daga watan Maris na 2024, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 19% a duk shekara daga ₦2,606 ($2) ) a shekarar 2023.
Amfani da Datar Airtel ya karu da kashi 25.4%, wanda ya karu daga 5GB a kowane wata zuwa 6.3GB a lokacin da ake nazarin sauyin bayanan.