Hukumar EFCC ta gurfanar da wani ɗan Chuba mai suna Liu Beixiang a gaban kotu da ke Ikoyi, a Jihar Legas, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya ga jami’in hukumar.
EFCC ta ce laifin ya faru ne a watan Disamban 2024, inda ake zargin Liu da yin ƙarya ga jami’in gwamnati yayin gudanar da aikinsa, wanda ya saɓa wa dokar hukumar.
- Mafarauta Sun Nemi Adalci Kan Kisan Mambobinsu A Edo
- Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu A Wani Sabon Hari A Filato
Liu ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi.
Lauyan EFCC ya roƙi kotu da ta saka ranar shari’a kuma a tura wanda ake zargin gidan gyaran hali.
Sai dai lauyan Liu ya ce sun riga sun miƙa buƙatar yin sulhu da kuma neman beli.
Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2025, domin samun rahoto kan sulhun, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi.













