Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta miƙa dalar Amurka $22,000 da ta kwato daga hannun wani dan damfarar yanar gizo mai suna Hakeem Ayotunde Olanrewaju ga hukumar FBI a Legas a ranar 17 ga Mayu, 2024.
Mai shari’a Nicholas Oweibo ya bayar da umarnin ne a ranar 15 ga Agusta, 2023, cewa a mayar da kuɗaɗen da aka ƙwato daga hannun Olanrewaju wanda aka yankewa hukuncin ɗaurin shekaru biyu bisa samunsa da laifin satar bayanan sirri da kuma yin sojan gona.
- Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo
- EFCC Za Ta Fara Amfani Da Fasahar Zamani Wajen Gano Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci
A wajen bikin miƙa kuɗin, muƙaddashin daraktan hukumar EFCC na shiyyar Legas, Michael T. Wetkas, ya jaddada aniyar EFCC na yaƙi da miyagun laifuka da kuma dawo da oda.
Jami’in shari’a na FBI Charles Smith ya godewa hukumar ta EFCC bisa haɗin kan da suka yi wajen kwato kuɗaɗen, yana mai jaddada mahimmancin irin wannan nasarar ƙwatowar ga ƴan kasuwar Amurka da abin ya shafa.
Taron ya samu halartar jami’an EFCC da na FBI da suka hada da shugaban hulɗa da jama’a na Legas, DCE Ayo Oyewole.