Domin hana duk wani tirjiya daga gwamnonin jihohi, hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) za ta fara bibiyan kudaden da ake tura wa kananan hukumomin kai tsaye nan da watan Nuwamba 2024.
Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa, Hakeem Ambali ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi da ta gabata.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Layuka A Gidajen Mai Za Su Ragu Idan ‘Yan Kasuwa Suka Fara Sayan Mai A Wajenmu – Dangote
Hakan ya kasance kamar yadda hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta tabbatar da aniyarta na sa ido sosai tare da bin diddigin yadda shugabannin kananan hukumomi ke kashe kudaden shiga daga asusun da gwamnatin tarayya ke warewa duk wata.
Wannan sabon ci gaba ya nuna wani gagarumin sauyi na aiwatar da ikon mallakar kananan hukumomi kamar yadda kotun koli ta ba da umarni da kuma gabanin wa’adin ranar 31 ga Oktoba da aka sanya wa jihohi su gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi.
A watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban kotun koli ta hannun babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, inda ta shigar da kara domin kalubalantar ikon gwamnonin na karba da kuma hana kudaden da gwamnatin tarayya ke yi wa kananan hukumomi.
Karar ta nemi hana gwamnonin jihohi rusa zababbun shugabannin kananan hukumomi tare da kafa kwamitocin riko.
Babban lauyan gwamnatin tarayya ya yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba da umarnin gudanar da zaben kananan hukumomi ta hanyar dimokuradiyya.
A ranar 11 ga Yuli, 2024, kotun koli ta zartar da hukunci da ke tabbatar da cin gashin kai na harkokin kudi na kananan hukumomi 774 da ke kasar nan.
Sai dai an samu jinkirin fara aiwatar da tsarin sakamakon dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi na tsawon watanni uku saboda damuwar da ta taso dangane da tasirinta na biyan albashi da kuma yadda za a iya gudanar da tsarin.
Har ila yau, a ranar 20 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta kafa hadakar kwamitin ma’aikatu mai mambobi 10 don aiwatar da hukuncin da kotun koli ta yanke kan cin gashin kan kananan hukumomi.
Mambobin kwamitin sun hada da ministan kudi, Wale Edun; babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN; ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu; Akanta-Janar na tarayya; Oluwatoyin Madein da gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso.
Sauran sun hada da sakatare janar na ma’aikatar kudi ta tarayya, Misis Lydia Jafiya, shugaban hukumar kula da rarraba asusun gwamnatin tarayya, Mohammed Shehu, da wakilan gwamnonin jihohi da na kananan hukumomi.
Babban aikin kwamitin dai shi ne, tabbatar da ganin an bai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu, tare da ba su damar gudanar da aiki yadda ya kamata ba tare da tsangwama daga gwamnatocin jihohi ba.
Kwamitin wanda sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya jagoranta, ya kammala tare da mika aikinsa a ranar 13 ga watan Oktoba.
A ranar Talatar da ta gabata ne wani bincike da jaridar The PUNCH ta gudanar ya nuna cewa akalla kananan hukumomi 164 a jihohi takwas ne har yanzu ba su gudanar da zabe ba, kuma akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta kwace kason kamar yadda kotun koli ta zartar.
A halin yanzu dai, shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ce hukumarsa za ta sanya ido a kan yadda ake gudanar da kasafin kudin daukacin kananan hukumomin kasar nan.
Olukoyede, a wata hira da aka buga a mujallar hukumar, wanda wakilinmu ya samu kwafinsa a ranar Lahadi, ya bayyana cewa hukumar EFCC za ta sanya ido kan yadda ake gudanar da kasafin kudin na dukkan kananan hukumomin kasar nan.
Ya koka da yadda gwamnatocin jihohi ke yin tasiri a kan albarkatun kananan hukumomin.
Shugaban EFCC ya ce hukumar ta fadada ayyukanta a fadin kasar nan. Ya kuma sha alwashin cewa duk wani jami’in karamar hukumar da ya karkatar da kudade za a kama shi kuma a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.
Shi ma shugaban kungiyar kananan hukumomi a Nijeriya, Aminu Kaita, ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da rabon kason kudaden kananan hukumomin daga asusun tarayya.
Kaita ya shaida cewa, “Muna aiki tukuro. Rana ta karshe shi ne Oktoba, kuma bai wuce ba tukuna. Don haka muna aiki a kan hakan.”