Connect with us

WASANNI

EUFA Za Ta Hukunta Kungiyar PSG

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA ta sake bude bincike kan yadda kungiyar kwallon kafa ta PSG ta Faransa ke kashe makudan kudade wajen siyan manyan ‘yan wasa a duk kakar wasa.

Wannan na zuwa ne bayan a cikin watan Yuni aka wanke PSG game da zargin ta da karya dokokin kashe kudade, amma UEFA ta ce, akwai bukatar sake duba lamarin.

PSG dai ta lale kimanin Euro miliyan 222 don kulla kwantiragi da dan wasan Brazil, Neymar, daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Sipaniya a cikin watan Agustan shekara ta 2017.

Sannan ta sake sayen Kylian Mbappe akan Euro miliyan 180 a cikin wannan kakar bayan ya shafe dogon lokaci a kan aro daga kungiyar Monaco, wato kungiyar da dan wasan ya girma tun yana dan karami

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai dai tuni ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki kungiyar PSG akan yanayin yadda kungiyar take kashe kudi kuma bayan akwai dokar yadda aka tsara kungiyoyi zasu kashe kudi wajen siyan ‘yan kwallo.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turan dai ta bayyana cewa idan har aka kama PSG da laifi tabbas za’a hukuntata ta hanyar hanana siyan ‘yan kwallo na tsawon shekara daya ko biyu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: