Sharfaddeen Sidi Umar" />

Faduwa A Kotun Koli: Ko Tambuwal Ya Dusashe Tasirin APC A Sakkwato?

A yayin da Kotun Koli ta tabbatarwa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kujerarsa a matsayin mutum mafi daraja ta daya a Jihar Sakkwato wanda zai ci-gaba da jagorantar al’ummar Jihar har zuwa kakar zaben 2023, a bayyane yake cewar jam’iyyar APC da magoya bayanta wadanda suka nunawa Tambuwal zazzafar adawa sun shiga cikin rudani da rashin makama.

Shan kaye a zaben farko da zaben raba gardama, sa ran karbar mulki ko soke zabe inma a kotun karar zabe, kotun daukaka kara da karshe a Kotun Koli wadanda duka suka yi watsi da karar APC da dan takarar ta Ahmad Aliyu a bisa ga rashin ingantattun hujjoji, abubuwa ne da ke tabbatar da shigar jam’iyyar a cikin yanayin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Gabanin fafatawar babban zaben 2019, mafi yawan magoya bayan jam’iyyar APC wadanda suka shiga cikin jirgin jam’iyyar sun yi ne da yakinin hakar su za ta cimma ruwa ta samun gagarumar nasara a zaben Gwamna da sauran kujeru musamman a bisa ga amintar su da zaman Sanata Aliyu Wamakko a matsayin jagoran siyasar Sakkwato wanda suke da amannar yana da karfin ikon azata ta zauna.

Wamakko wanda ya jagoranci al’ummar Jihar Sakkwato mulkin tsayin shekaru takwas, ya samu cikakkiyar damar jan zarensa yadda yake so tare da hanawa ‘yan adawa sararawa tare da kashe kaifin adawa a wa’adin mulkinsa ba tare da ba su damar numfasawa a siyasance ba. Hasalima bayan canza murhun siyasar Tambuwal daga APC zuwa PDP a ranar 1 ga watan Agusta 2018, Wamakko ya fito fili ya jajantawa Gwamnan domin a cewarsa ya cancanci a tausaya masa ganin ya fita daga jam’iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari da shi Wamakko yake ciki wanda a tunanin sa a wancan lokacin lissafin siyasa ya kwace wa Tambuwal.

Akasin hakan, Tambuwal wanda masu fashin bakin lamurran siyasa suka bayyana a matsayin nagartaccen dan siyasa wanda ke da kwarewa, gogewa da sanin ciki da wajen siyasar ci-gaban al’umma, ya hanga ya hango tarkuna da shingayen da aka dana masa ya kuma tunkare su tare da samun nasarar tsallake su ta hanyar lakantar matsalolin siyasa da hanyoyin warware su kamar yadda jama’a suka shaida da kan su.

Babban zaben 2019 zabe ne da aka yi zargin jam’iyyar APC, jiga-jigan ta da Gwamnatin Tarayya suka yi amfani da sojoji, ‘yan sanda da jami’an EFCC domin ganin ta ko wace irin hanya PDP ba ta kai labari ba kamar yadda shi da kansa Tambuwal ya bayyana jim kadan bayan samun nasararsa wadda ya ta’allaka ga Allah madaukakin Sarki wanda ya kaddare shi da samun galaba. A cewarsa duk abin da ake yi domin ganin ya fadi zabe an yi amma a bisa ga goyon baya da addu’o’in da al’ummar Jihar suka dukufa a kai, Ubangiji ya kalle su da idon Rahama ya share masu hawaye.

A zaben wanda a bayyane guguwar Buhari ta yi matukar tasiri, APC ta shiga gaban PDP a kujerun Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki ta Jiha domin kuwa APC ta na da ‘Yan Majalisar Dattawa uku tare da ‘Yan Majalisar Wakilai tara, a yayin da PDP ke da biyu. Bugu da kari a Majalisar Dokoki APC na da 16, PDP kuwa na da 14. Sai dai jam’iyyar PDP ta samu Sanata daya bayan da kotun daukaka kara ta karbe kujerar daga APC haka ma PDP ta samu gagarumar nasarar karbe kujera daga hannun APC a zaben cike gurbi da Hukumar Zabe ta gudanar kwanan nan bayan soke zaben Dan Majalisar Wakilai a Mazabar Sokoto ta Arewa da Sokoto ta Kudu.

Yadda jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasara a zaben na cike gurbi ciki har da Dan Majalisar Wakilai na Isa-Sabon-Birni wanda ya dawo kan kujerarsa da ‘Yan Majalisar Dokoki biyu da suka sake dawowa kan kujerun su a Binji da Sokoto ta Arewa ta (2) da yadda dan takarar APC a Binji ya koma PDP kwana uku kacal kafin zabe tare da janye takararsa abubuwa ne da suka tabbatar da rauni da karya lagon APC da Tambuwal da jam’iyyarsa ta PDP suka yi a Sakkwato.

Karara zaben wanda Sanata Aliyu Wamakko ya yi kiran musamman ga magoya bayansa da su tabbatar ‘yan takarar su sun kai labari a fafatawar wadda aka yi kare jini biri jini, APC ba ta sha da dadi ba domin jama’a sun yi yi wa ‘yan takarar PDP ruwan kuri’u wanda a fili hakan ya nuna cewar hatta zaben 2019 da ya gudana, ‘yan takarar da suka lashe zabe a inuwar APC, sun shiga cikin guguwar rigar Buhari suka kai bante domin kuwa a wannan zaben karfin kowa ya bayyana a fili tamkar kibar doki.

Kokuwar da Tambuwal ya yi da Wamakko da babban kayen da ya yi masa lamari ne da za a iya cewa ya zama sila ko mafarin karya lagon babban jigon adawarsa APC a Jihar wanda magoya bayansa ke ganin ba za a kara da shi a kai labari ba. Don haka a yanzu da ake ganin Mutawallen Sakkwato ya dusashe siyasar Sarkin Yamman Sakkwato, dimbin jama’a da masu fashin bakin lamurran siyasa na da ra’ayin Tambuwal ya kai cikakken gwarzon dan siyasa wanda ya jagoranci canza fasalin siyasar Jihar Sakkwato musamman bisa ga yadda dubban daruruwan Sakkwatawa suka jaddada amintaccen kuma cikakken goyon bayansu ga Tambuwal da Gwamnatinsa.

Tun bayan karewar wa’adin mulkin Attahiru Dalhatu Bafarawa a 2007, Wamakko a matsayin Gwamna zuwa matsayin Sanata a 2015 zuwa Agusta 2018 da suka raba gari da Tambuwal ya samu cikakkiyar damar sawa da fitarwa tare da umurtar yi ko bari a dukkanin lamurran siyasa da na Gwamnatin jihar Sakkwato, to amma a yau tuni wannan ya zama tarihi a bisa karbe kambun jagorantar siyasar Sakkwato da Tambuwal ya yi.

A kan rashin cikar mafalkin APC na samun damar dora dan takarar su a matsayin Gwamna, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir wanda ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa ya bayyana takaici da jin zafin faduwa shari’a a Kotun Koli yana cewar hukuncin ya tsorata tare da razana su matuka.

Sanata Gobir wanda ya bayyana hakan a madadin APC kan hukuncin ya ce “Ko kadan ba mu taba tsammanin wannan hukuncin ba, mun dauka alkalan za su yi mana adalci amma kuma hakan ba ta samu ba. Don haka mun karbi hukuncin da kyakkyawar manufa, kuma ko shakka babu Sakkwato Jihar APC ce babu wanda zai yadda cewar PDP ta lashe zabe.” Kamar yadda ya bayyanawa manema labarai bayan gangamin taro a gidan Sanata Wamakko.

Babban jigon dan siyasa kuma Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato Hon. Abubakar Zaki Bashire ya bayyana zaben na cike gurbi a matsayin ‘yar manuniyar da ta nuna yadda zaben 2023 zai zama ya kasance ba tare da Buhari ba ballantana guguwarsa domin a yayin da Wamakko ya gudanar da babban gangamin yakin neman zabe tare da tarbon dawowarsa daga Abuja da dubun-dubatar jama’a tare da ikirarin Jihar Sakkwato tashi ce, sai ga shi Sakkwatawa sun nuna inda alkiblar siyasar su ta karkata wanda hakan ya kara tabbatar da Tambuwal a matsayin wanda Sakkwatawa suka aminta da shi.

Hon. Bashire wanda, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tambuwal, ya bayyana cewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu gagarumar karbuwa ga al’ummar Jihar Sakkwato a bisa ga zamansa dan siyasa mai dattako da sanin ya kamata wanda ya himmatu wajen samar da ci-gaba mai ma’ana ga al’umma.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Gwamna ne wanda ya jagoranci gudanar da ingantacce, karbabbe kuma amintaccen mulki nagari a shekaru kusan hudu na mulkinsa. Gwamnatinsa wadda ta fifita bunkasa rayuwar al’umma ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa sha’anin kiyon lafiya, inganta aikin gona, shimfida hanyoyin mota, kyautata tsaro, cusa da’a da tarbiya a tsakanin al’umma da share hawayen marasa galihu wadanda Gwamnati ke baiwa alawus din N6, 500 a kowane wata tare da biyan albashi kan kari a daidai lokacin da ma’aikata ke bin wasu Gwamnatoci bashin wata da watanni. Haka ma Tambuwal ya biya kudin fansho da garatuti na sama da biliyoyin naira tare da fara biyan albashi mafi karanci na naira dubu 30, 000 daga watan da ya gabata tare da bunkasa sha’anin ilimi a karkashin dokar daukin gaggawa wadda aka kashe bilyoyin naira.

A bisa ga canza shekar Tambuwal zuwa PDP tare da samun nasara a lokacin da ake ganin kuskuren siyasa ne fita daga jam’iyyar Shugaba Buhari zuwa wata jam’iyya da yadda ya yi wa abokan adawa bugun a kawo wuka a zaben farko da mummunan kaye a zaben raba gardama da nasararsa daya, biyu har uku a kotuna daban-daban da suka tabbatar da zaben sa da yadda ya jagoranci jam’iyyar PDP ga samun nasara a zaben cike gurbi na kujerun Majalisar Wakilai biyu da Majalisar Dokoki biyu da zabensa a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya da zabensa a matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, abubuwa ne da ke tabbatar da zaman Tambuwal dan siyasa mai matukar sa’a da nasibi wanda ya shiga gaban abokan adawawarsa da suka sha alwashin yi masa ritaya a siyasance.

Exit mobile version