Rabe-raben Hassa da
Ci gaba: Mataki na Biyu na Hassada:
Shi ne mutum ya so wata ni’ima ta gushe daga hannun wani saboda yana fatan ta koma wurinsa. Wannan nau’in hassada yana haɗe da kwaɗayi da son kai, domin mai irin wannan hali yana ganin cewa shi ne ya cancanci wannan ni’ima fiye da wanda yake da ita.
Misalin Irin Wannan Hassada:
Mutum yana so wani ya rasa matsayinsa ko shugabancinsa saboda yana fatan shi ya maye gurbinsa, ko wani ya riƙa fatan wani ya yi asarar dukiyarsa don shi ya gaji wannan dukiya, ko wani ya so wata mace ta rabu da mijinta saboda yana son ya aure ta, ko wani ɗalibi ya so a kore wani daga makaranta don shi ya karɓi gurbin sa.
Wannan matakin hassada yana nuna babban matsayi na mugunta da rashin tausayi. Mai irin wannan hali ba kawai yana jin haushin ni’imar wani ba, har ma yana ƙoƙarin ganin ya mallake ta.
Alamomin Wannan Hassada:
Mutum mai irin wannan hassada yana da wasu alamu da ke bayyana shi:
• Jin tsananin kwaɗayi da kishi a kan wata ni’ima.
• Yana tunanin cewa shi ya fi cancanta da wannan alheri.
• Ƙoƙarin hana mai wannan ni’ima jin daɗin rayuwarsa.
• Idan wannan ni’ima ta gushe daga hannun wanda yake da ita, sai ya ji daɗi kuma ya natsu.
• Yana iya ɗaukar matakai na sharri don ganin ya mallaki abin da ba nasa ba.
Misalan Wannan Hassada:
1. Hassadar Fir’auna a Kan Annabi Musa (AS):
Fir’auna ba ya son aiken da Allah Ya yi wa Annabi Musa (AS) ba, domin yana tsoron cewa mulkinsa zai ƙare. Ya so cewa wannan matsayi na shugabanci da iko ya kasance a gare shi kawai.
Allah Ta’ala Ya ce:” Fir’auna kuma ya ce: ‘Ku bar ni in kashe Musa, kuma ya je ya kira Ubangijinsa! Lallai ni ina tsoron ya canza addininku, ko kuma ya bayyana ɓarna a cikin ƙasa.'” Suratu Gãfir aya ta 26.
Fir’auna bai so wani ya sami iko ko shugabanci sai shi, don haka ya so ya kashe annabi Musa (AS) domin mulkinsa ya dore.
2. Hassadar Ƙuraishawa ga Annabi Muhammad (SAW):
A lokacin da Manzon Allah (SAW) ya bayyana da’awarsa, manyan shugabannin Ƙuraishawa sun ji haushin hakan, domin suna son a ce su ne kawai suka mallaki wannan matsayi na shugabanci da daraja. Allah Ta’ala Yana cewa “ Yanzu su ne suke raba rahamar Ubangijinka (ta annabi)? Mu ne muka raba musu arziƙinsu a rayuwar duniya. Mu muka ɗaukaka darjojin sashinsu a kan sashi, don wani sashi ya riƙi wani sashi mai yi masa hidima. Rahamar Ubangijinka kuma ita ta fi abin da suke tarawa na duniya.” Suratuz-Zukhruf aya ta 32.
Illolin Wannan Hassada:
Rashin Yarda da Ƙaddarar Allah: Mutum mai irin wannan hassada yana ƙin yarda Allah Ya raba ni’imomi. Yana jin cewa shi ya fi cancanta da wata ni’ima fiye da wanda yake da ita. Wannan yana nuni da ƙarancin imani.
Haddasa Gaba da Rikici: Wannan nau’in hassada yana jawo matsaloli a cikin zamantakewa. Idan mutum yana da burin hana wasu cin gajiyar ni’imar da Allah Ya ba su, to hakan yana haifar da gaba, kishi, da yaƙe-yaƙe a cikin al’umma.
Rashin Albarka a Rayuwa: Allah Ba ya albarkantar da wanda yake da zuciyar hassada. Mutumin da yake son ya hana wani alheri don shi ya mallake shi, sau da yawa ba zai kai ga hakan ba, kuma ko da ya samu, ba zai sami albarka a ciki ba.
Ruɗewa da Rashin Hankali: Mai irin wannan hassadar baya samun kwanciyar hankali. Yana jin kishi da tsananin damuwa idan wani yana cikin ni’ima. Wannan yana iya haifar da ciwon zuciya, matsanancin damuwa, da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp