Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta sanar da saukar farashin kayayyaki a sassan kasar nan a cikin watan Disamba 2022, irinsa na farko a cikin watanni 11 da aka shafe ana fama da tsadar kayayyaki musamman na abinci.
Alkaluman da NBS ta fitar, ya ce tsadar rayuwar ta ragu zuwa kashi 21.34 daga kashi 21.47 da aka gani a watan Nuwamba 2022, yayin da tsadar kayayyakin masarufi ya sauka daga kasha 24.13 zuwa kashi 23.75, duk da cewa akwai matsalar rashin tsayuwar farashi a wasu yankuna na kasar nan.
- Akwai Hatsarin Gaske Mika Mulkin Nijeriya A Hannun Tinubu ko Obi – AtikuÂ
- A Boye DSS Ta Ayyana Cafko Emefiele – Femi Falana
Saukar farashin a cewar NBS, ya zo ne cikin watan na Disamba dai-dai lokacin da jama’a ke shirin fara bukukuwan Kirsimati da na sabuwar shekara.
Rahoton na NBS ya ce kayayyakin da farashinsu ya sauka sun kunshi na abinci da nau’ikan ababen sha sai kuma farashin sufuri da shi ma ya sauka lamarin da ya samar da sassauci ga tsadar rayuwar da jama’a ke fama da shi.
Rahoton na NBS dauke da wannan alkaluma na zuwa ne a dai-dai lokacin da kwamitin manufofin kudi na babban bankin Nijeriya (CBN) ke shirin gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki irinsa na farko cikin shekarar nan, ganawar da ake sa ran ta tabo hanyoyin magance matsalar tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyakin da al’ummar kasar nan masu karamin karfi ke fama da shi.