Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a Mohammed Idris, ya sanar da cewa, farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan, ya dogara ne kan bunƙasa fannin makamashi, musamman ta hanyar yin amfani da dabarun zamani.
Ya bayyana haka ne a taro gabatar da Lakcha na shekara-shekara karo na 8 da Mujallar ƁalueChain ta gudanr a Abuja.
Ministan ya bayyana cewa, Gwamnatin Shuagabn Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ci gaba da ɗaukar matakai, domin sake farfaɗo da fannin na makamashi, wanda ya sanar da cewa, Gwamnatin za ta yi hakan ne, na dogon zango.
- Karin Kasashe Masu Tasowa Sun Shiga Aikin Sarrafa Harkokin Tattalin Arzikin Duniya
- Firaministan Sin Zai Gudanar Da Tattaunawa Ta “1+10” Da Shugabannin Manyan Hukumomin Tattalin Arziki Na Duniya
Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta mayar da hankali wajen ganin ana bunƙasa fannin samar da Iskar Gas, samfarin CNG, wanda ya sanar da cewa, hakan na daga cikin daburun gwamnatin na samar da ingantance kuma tsaftataccen Iskar ta CNG
“Wannan ba wai kawai tari ne na samar da makamashi ba, har da ma samar da ɗauki na kai tsaye ga fannin sufuri da samar da kaya,” Inji Ministan.
Ya ci gaba da cewa, bisa dokar samar da wutar lantarki da kuma ƙulla haɗaka a tsakanin gwamnatin jihohi da gwamnatin tarayya, gwamnatin na da aniyar tabbatar da ana cin gajiyar damar da ake da ita a ɓangaren masu zuba jari.
A cewarsa, bisa ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa yin amfani da kayan da ake sarrafawa a ƙasar nan, gwamnatin ta himmatu wajen ganin cewa, fannin na makashi na ƙasar ya kai babban mataki a ɗaukacin faɗin Afirka, musamman a ɓangaren zuba jari.
Ya ƙara da cewa, waɗannan sauye-sauyen manyan ne, waɗanda kuma a wani lokacin, suka kasance masu ƙalubale.
Shi kuwa a na sa jawabin a wajen taron Babban Sakatare na Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur Dakta Emeka Ɓitalis Obi ya bayyana cewa, fannin na makamashi ba wai kawai ana amfani da shi a rayuwar yau da kulum bane, amma wani babban ginshiƙi ne, da ke ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasa da samar da ayyukan yi da daidaita al’amura da kuma ƙara wanzar da tsaro.
Shi kuwa a na sa jawabin a wajen taron mawallafin Mujallar kuma Babban Edita Ɓaluechain Musa Bashir Usman ya sanar da cewa, fannin makamashi na ƙara matsawa daga ɓangaren fasahar kimiyyar zamani da ɓangaren tattalin arziki ko kuma ɓangaren siyasa, wanda ya sanar da cewa, akwai buƙatar a tabbatar da ana tattaunawa kan yadda za a citar da fanning aba a ƙasar nan.
Dalilin Ci Gaba Da Fuskantar Ƙalubale A Fannin Kiwon Zuma A Nijeriya –Ƙwararre
Wani ƙwararre a fannin kiwon Zuma a Jihar Edo, Mista Abudu Inanigie ya bayyana cewa; ana samun ɗimbin kuɗaɗen shiga a fannin kiwon Zuma duk da cewa, akwai manyan ƙalubale a fannin.
Ya ce, matuƙar masu sha’awar shiga fannin suka bi ƙa’idar kiwon nata, za su iya samun kuɗaɗen shiga masu yawa.
Sai dai, ya yi nuni da cewa; mutane da dama na tsoron shiga fannin, sakamakon wahalhalun da ke cikinsa, musamman na tsoron harbin zumar.
Ya ƙara da cewa, yana samun annashawa a kiwonta, wanda ya ce fanni ne mai sauƙin gaske a gare shi.
Abudu, wanda ya ke gonar kiwonta a ƙauyen Auchi da ke yankin Ikabigbo na Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma a jihar ta Edo ya ƙara da cewa; yana kuma koyar da mutane kiwon zumar.
A cewarsa, kiwonta kamar sauran fannonin aikin noma, akwai ƙalubale, wanda hakan ya sanya mutane suke guje wa kiwon nata.
Mista Inanigie ya yi nuni da cewa, samun gonar da aka shuka Fulawa, na ɗaya daga cikin ƙalubale a fannin, domin kuwa, zuma aba ce da ke da matuƙar buƙatar filawa, musamman duba da cewa; ta haka ne kawai, za su iya samar da zumar.
“Har yanzu a ƙasar nan, ba a rungumi yin kiwonta a zamance ba, duba da cewa; mutane ‘yan ƙalilan ne kawai a ƙasar suka rungumi yin ta a zamanance .”
Ya yi nuni da cewa, yawan samun masu sayar da gurɓatacciyar zumar a ƙasar, na ɗaya daga cikin ƙalubalen da fannin ke ci gaba fuskanta a ƙasar, wanda kuma hakan ya sa mutane har yanzu, ba su yi ammanar cewa; ana samun ingantacciyarta a ƙasar nan ba.
“Saboda samun gurɓatacciyar zuman ne, mutane ba sa iya tantacewa tsakanin ingantacciyar da kuma wadda aka gurɓata,” in ji shi.
Bugu da ƙari, ya bayyana cewa; masu sana’ar, ba sa samun wani rancen kuɗi ko samun kayan kiwonta daga wurin gwamnati.
Kazalika, ya bayyana cewa; akwai kuma ƙalubalen rashin wayar da kan jama’a, kan alfanun da ake samu a fannin da rashin jawo matasa, domin shiga cikin fannin da rashin tsaro tare da kuma satar zumar da wasu ke yi.
Rashin Sama Wa Fannin Kasuwa:
Ya ce, ana da buƙatar zuma matuƙa a ƙasar nan, amma har yanzu, ba ma iya samar da wadatacciyarta, domin mutane ƙalilan ne a cikin fannin.
“Matuƙar mutane suka san cewa, mai sana’arta na samar da ingantacciyarta, za su riƙa zuwa suna saye,” a cewarsa.
Matakin Farko Ga Wanda Zai Fara Yin Kiwonta:
“Ana buƙatar ya fara kiwata ‘yar kaɗan tare kuma da jurewa ci gaba da yin kiwon har ta kai ga ta faɗaɗa, in ji ƙwararren.
Ya ƙara da cewa, ana kuma buƙatarsa ya kasance ya samu ilimin yin kiwonta tare da kuma fahimtar yadda halayenta suke, domin ya samu kai wa ga cin nasara.
Ya ce, ana kuma buƙatar ya samu kayan da zai sanya a jikinsa, domin ya bai wa kansa kariya daga harbinta da tanadar safar hannu da sauran kayan aiki.
“Za ka iya gina mata ɗakin kwana, wato wani ɗan akwati; sai ka rataye shi a kan bishiya”.
“Haka nan, za ka iya samun wani wajen da yake da fulawa, wanda hakan zai sa ta riƙa tsotsar furen da ke jikin fulawar, domin ta riƙa samar da zumar, kuma ana son wajen ya kasance wanda za ka iya riƙa sa mata ido.
“Za ka kuma iya samar mata da ɗakunan kwana, har zuwa huɗu kana kuma ci gaba da bibiyar ta, wanda hakan zai sa ta saba da kai, musamman duba da cewa; zuma na yin harbi a-kai-a-kai”.
Farashinta: A batun hada-hadar kasuwancinta, mai sana’ar babu ruwansa da wani batun ƴan na kama, domin mai sana’ar zai iya sayar da zumarsa, kai tsaye, ba tare da wata tangarɗa ba.
“Farashinta ya sha ban-ban, domin mai sana’ar na iya sayar da ita kai tsaye ga kamfanoni ko kuma ga ɗaiɗaikun mutane.
“Kwalbar zuma mai nauyin 50cl, ana sayar da ita daga naira 6,000 zuwa Naira 7,000; haka ana sayar da kwalba mai nauyin 75cl daga naira 9,000 zuwa Naira 10,000, inda kuma a wani wajen ake sayar da lita ɗaya, kan naira 15,000, ko sama da haka.
Lita 10 ta zuma, ana sayar da ita kan kimanin naira 150,000 ko sama da haka, inda kuma lita huɗu ake sayar da ita, kan kimanin naira 40,000.
Ya sanar da cewa, har yanzu wasu masu sana’ar na yin kiyonta ta hanyar gargajiya, amma hanyar da ta fi da cewa na kiwonta shi ne, rungumar yin ta ta hanyar gargajiya.














