An haifi Zaynab Alkali a shekarar 1950 a Tura-Wazila da ke Jihar Borno. Daginta Musulmi ne da suka fito daga Tura-Wazila da ke Jihar Borno a Nijeriya, daga baya kuma suka koma wani kauyen Kirista a Jihar Gongola, inda a nan ta girma.
Ta fara karatun firamare a makarantar firamaren ‘yammata ta kwana dake Waka, Biu, Daga baya kuma ta tafi zuwa Makarantar Sarauniya, llorin, Jihar Kwara. Daga nan ne kuma ta tafi Jami’ar Bayero inda ta kammala digirinta na biyu a shekarar 1973. Daga nan ta samu digirin digirgir a fannin adabin Afirka da turanci a shekarar 1979 a wannan jami’a, sannan ta zama shugabar makarantar kwana ta ‘yan mata ta Sakera.
- Tinubu Ya Sake Nada Farfesa Sheshe Shugaban Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano
- Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ba Za Ta Samu Wani Sabon Bashi Daga Bankin AfDB Ba -Farfesa Oyebanji
Ta kasance Babbar Malama a fannin Turanci a Jami’ar Maiduguri; Jihar Borno. Daga nan ta bar Jami’ar Maiduguri zuwa Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko da ke Abuja na tsawon shekaru uku kafin ta tafi Jami’ar Jihar Nasarawa, ta yi shekaru 22 a Jami’ar Maiduguri, sannan ta yi wasu shekaru a Jami’ar Bayero ta Kano.
Ta auri Farfesa Muhammad Nur Alkali tsohon mataimakin shugaban jami’a kuma Allah ya albarkace su da samun ‘ya’ya shida.
Ana kallon Zaynab Alkali a matsayin mace ta farko da ta fito daga Arewacin Nijeriya, mamba a Kungiyar Marubuta ta Najeriya, Tsohuwar shugabar ANA ce reshen Jihar Borno.
Ta yi karatu a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi inda ta koyar da rubuce-rubucen kere-kere
Zaynab Alkali ta zama shugabar tsangayar fasaha a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. Sannan kuma ta kasance shugabar makarantar kwana ta Shekara, dake Kano daga shekarar 1974 zuwa 76.
Ta yi aiki a matsayin mataimakiyar malama a Bayero ta Kano, ta kasance Malama a Jami’ar Maiduguri a daga 1981 zuwa 83.
Zaynab Alkali, Malama ce kuma kodineta a fannin Turanci a kwalejin Janar, Modibbo Adama, Yola daga 1984 zuwa 85.
Ta kuma yi aiki a matsayin Babbar Malama a fannin Turanci a Jami’ar Maiduguri, a 1985
Ta auri Farfesa Muhammad Nur Alkali tsohon mataimakin shugaban jami’ar Maiduguri
Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) ta karrama ta da lambar yabo, a 1985.