Firaministan kasar Malaysia, Dato’ Seri Anwar, ya yi hira da wata wikiliyar CMG a kwanan baya, inda ya ce, kasar Sin na son fahimtar al’adu na sauran kasashe, da tunaninsu na musamman. Wadannan abubuwa tushe ne ga zumuncin da ya kasance tsakanin kasashen 2, gami da sanya Sin zama aminiyar kasar ta Malaysia.
Yayin tattaunawarsa da wakiliyar CMG, Malam Dato’ Seri Anwar ya ambaci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigar da su cikin kasuwannin kasar Sin na CIIE, da ya kan gudana a birnin Shanghai na Sin, inda ya ce, wannan biki ya nuna nasarorin da kamfanonin kasar Sin suka samu, da dimbin kayayyakin kasar Sin masu inganci. Ban da haka, a cewar jami’in Malaysia, bikin CIIE ya zama wani muhimmin dandali ga kasashe daban daban, don su nuna da tallar kayayyakinsu ga jama’ar kasar Sin, da kuma samar da damar ciniki. Hakan ya nuna yadda ake kokarin dabbaka tunanin al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
- Manyan Bankunan Kasa Na Sin Da Nijeriya Sun Sabunta Yarjejeniyar Musayar Kudi
- An Jinjina Wa Tawagar NPA Kan Samun Nasarar Sayar Da Danyen Mai Da Takardar Naira
Haka zalika, Malam Anwar ya ce, kasar Sin ta tsaya kyam kan tattaunawa tare da sauran kasashe ta sahihiyar hanya, lamarin da ya kaddamar da sabon salon cudanya tsakanin kasashe daban daban.
Ban da haka, kasar Sin tana giramama kasashen Afirka, da na kudu maso gabashin Asiya, da wadanda suke nahiyar Amurka, da dukufa wajen tinkarar sauyawar yanayin duniya, da kokarin samar da gudunmawa ga burin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya ta hanyar aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, in ji firaministan kasar Malaysia. (Bello Wang)