A jiya Jumma’a 11 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci taron shugabannin Sin da kasashen ASEAN karo na 25, a birnin Phnom Penh, babban birnin kasar Cambodia. Taron da ya samu halartar shugabannin kasashen ASEAN, da Sakatare-Janar na kungiyar.
A jawabin da ya gabatar, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar ASEAN da fifiko a fannin diflomasiyya da makwabciyarta, kuma tana son mai da hankali kan samun ci gaba, da yin hadin gwiwa tare da ASEAN, da raba damammaki, da fuskantar kalubale tare, da gina al’ummar Sin da ASEAN mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
A nasu bangaren, shugabannin kasashen kungiyar ASEAN sun bayyana cewa, dangantakar ASEAN da Sin ita ce mafi inganci, a tsakanin abokan huldar shawarwari na ASEAN, inda ta zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin. Kuma suna son yin kokari tare da kasar Sin, wajen kara samun damar yin hadin gwiwa, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin ASEAN da Sin.
Taron ya zartas da wasu takardu da dama, wadanda suka hada da sanarwar hadin gwiwa don tunawa da cika shekaru 20 da sanya hannu kan sanarwar ayyukan bangarorin da suka shafi tekun kudancin kasar Sin da sauran su. (Mai fassara: Bilkisu Xin)