Daga Khalid Idris Doya,
Shiyya ta goma sha biyu, ta hukumar kiyaye hatsaruka kan hanyoyin kasar nan (FRSC), ta bayyana cewar, kotun tafi da gidan-ka ta hukumar a rukunin zaman ta na farko a garuruwan Bauchi, Toro, Azare, da Bara ta kama masu laifi guda dari da hamsin da bakwai (157) wadanda aka gurfanar da su a gaban kuliya.
Wannan bayani ya na dauke ne cikin wata sanarwa da hukumar ta kiyaye hatsaruka, wanda jami’in ta ACM Rotimi T. Adeleye ya sanya hannu kuma aka rarraba wa manema labarai a garin Bauchi shekaran jiya.
A cewar sanarwar, masu laifuka 145 an yi masu hukunce-hukunce kan laifuka daban-daban dangane da sufuri kan hanyoyi, yayin da kotu ta sallami guda goma sha-biyu daga cikin su.
“Daga gefe guda kuma, hukumar ta lura da wasu majibantan hanyoyi da suke aikata ba daidai ba. Wadannan kamfanoni ko hukumomi masu ayyukan safara, hukumar za ta zayyana masu ka’idojin safara kan hanyoyin kasar nan. Za a sanar da ofisoshin wadannan kamfanoni ko hukumomi kamar yadda ya dace.”
Sanarwar ta cigaba da cewa, “Rashin sanya na’urar gwajin tafiya akan hanya, dibar kaya fiye da kima da matsanancin gudu akan hanya su ne mafi munin laifuka da masu safara akan hanyoyi ke aikatawa. Wannan hukuma ta na kira ga masu tuki akan hanyoyi da su rika kiyaye dokokin safara domin kiyaye lafiyar su, hadi da masu amfani da hanyoyi.
“Ya na kuma da muhimmanci matuka da ka’idojin kariya daga cutar sarke numfashi (Korona) kamar amfani da Amawali, Kula da Tazara Tsakanin mutum-da-mutum, da wanke hannaye yayin tafiye-tafiye”.
Hukumar ta kiyaye hatsaruka ta yaba matuka-gaya yadda matuka ababen hawa suke kiyaye dokokin safara, musamman a lokutan shagulgula, hadi da hadin kai da masu safara suke baiwa hukumar ta kiyaye hatsaruka a yayin gudanar da ayyukan ta a shekara da ta gabata, husasan la’akari da zaman kotun tafi-da-gidanka a wannan shiyya.
Sanarwar ta hukumar, ta shawarci ‘yan-kasuwa, musamman masu tsuguni-tashi da su kauracewa gefen hanyoyi domin baiwa hanyoyin hakkokin su, musamman a lokutan shagulgulan al’adu ko addini domin kiyaye faruwar hatsaruka, kamar yadda hukumar ta ke jaddada jajircewar ta kan fadakar da al’umma.