Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da manyan shugabannin jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomi 44 na jihar, sun amince da sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar a zaben 2027.
Ganduje ya sanar da hakan ne bayan jerin tarukan shawarwari da ya gudanar da shugabannin jam’iyyar a gidansa da ke Kano, yana mai cewa tattaunawar na da nufin ƙarfafa haɗin kai da tsare-tsaren jam’iyya kafin babban zaɓe mai zuwa.
- Jami’an APC 3 A Jihar Zamfara Da Aka Dakatar Sun Maka Jam’iyyar A Kotu
- Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu
A jawabinsa, Ganduje ya ce burinsu shi ne tabbatar da cikakken zaman lafiya da daidaito a jam’iyyar daga mataki na ƙasa zuwa na sama, tare da nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Tinubu. Ya umarci shugabannin jam’iyya a matakan ƙananan hukumomi da mazaɓu da su tabbatar da buɗe ofisoshin APC a kowane yanki domin karɓar sabbin mambobi.
Ganduje ya kuma bayyana cewa za a ƙara ƙaimi a aikin rajistar mambobin jam’iyya ta hanyar amfani da tsarin zamani na diigital. Don haka, kowace ƙaramar hukuma za ta tura ma’aikatan ICT guda uku da aka horar domin jagorantar aikin, tare da niyyar faɗaɗa yawan mambobin jam’iyyar kafin zaɓen 2027. Haka kuma ya ja hankalin mambobi su bi ƙa’idojin INEC ta hanyar tabbatar da cewa dukkan masu shekaru 18 da haihuwa sun yi rijistar zabe bisa tsarin da ake gudanarwa a fadin ƙasa.
Jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci taron sun haɗa da tsohon Gwamnan Kano Kabiru Ibrahim Gaya, da ɗan majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, da ɗan takarar gwamna na 2023 Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo, Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas da sauran fitattun shugabannin jam’iyyar a Kano.
Sai dai ba a hango mataimakin shugaban majalisar dattawa ba Bari Jibrin da ƙaramin ministan gidaje Yusuf Ata ba, wanda wannan ta ƙara haska cewa akwai ɓarakar da zata iya raba jam’iyyar gida biyu a zaɓen 2027.














