‘An Gano Wasiƙun Soyayya Da Obama Ya Rubuta Wa Budurwarsa’

Mista Obama da Aleɗandra Mcnear, wanda Obama ya hadu da shi a California, ne suka rubuta wasikun.

An gano wasu wasiƙu da tsohon shugaban ƙasar Amurka Barrak Obama ya rubuta wa budurwarsa, tsohon suhagabn ya rubuta wasiƙar ne shi da wani abokinsa mai suna Aleɗandra Mcnear, wani matashi das u haɗu das hi a Jihar Caliponia.

Wasu daga cikin wasiƙun sun nuna ƙalubalen da tsohon shugaban Amurka ya fuskanta daga farko, a lokacin yana aikin da ba ya ƙauna domin kawai a ci gaba da rayuwa.

An wallafa wasikun ne kwanan nan a wani ɗakin karatu na Rose da ke jami’ar Emory da ta tsaya a shekarar 2014.

“An rubuta wasiƙun da kyakkyawan rubutu, kuma sun bayyana ba’asi da wani matashi ke yi na neman sani da kuma neman sanin asalinsa,” in ji Daraktan ɗakin karatun.

“Sun nuna irin abubuwan da ɗalibanmu suka fi damuwa da su, kuma ɗalibai a ko ina suke fuskanta.”

A wata mahangar kuma, an ruwaito cewa, an rubuta wasiƙun ne tsakanin shekarar 1982 zuwa 1984, shekara biyar kafin Mista Obama ya fara zuwa zance gun matar da ya aura daga baya, wato Michelle.

A ɗaya daga cikin wasiƙun na farko-farko, ya rubuta cewa: “Ina da yaƙinin cewa kin sani ina kewarki, kuma na damu da ke matuƙa, yardar da na yi da ke ta kai zurfin teku, kuma soyayyata (gareki) na da yawa.”

Amma soyayya daga nesan bai dace ba. A shekarar 1983, ya shaida mata: “Ina yawan tunaninki, duk da cewa a ruɗe nake game da yadda nake ji a rai na.”

“Kamar ba za mu taɓa so abin da ba za mu iya samu ba, wannan ne abin da ya haɗa mu, wannan ne abin da ya raba mu.”

A wata wasikar, matashi Obama ya yi rubutu yadda abokin nashi ke neman yin aure ko kuma karɓar ragamar kamfanonin gidansu.

Amman domin an haife shi a Hawaii, mahaifi daga Kenya, kuma domin ya yi yawancin shekarun yarintarshi a Indonesiya, ya ji kanshi daban.

“Dole na ce na yi fama da hassada,” in ji shi.

“Na samu kaina a wani halin da babu matsayi, tsari ko kuma al’ada wadda za ta tallafa mini, a iya cewa an yi mini zaɓin bin wata hanya ta daban ne.

“Hanya ɗaya da zan iya bi in rage raɗaɗin kaɗaitar da nake ita ce in karɓi al’adu da matsayi-matsayi sannan in mayar da su, ni kuma in zama na su, amma abin bai yi sauƙi ba.”

A matsayin shi na ɗalibin da ya kammala karatun Digiri a shekarar 1983, ya koma Indonesiya in da ya girma, ya gane cewa shi ya zama baƙo a wannan ƙasar .

“Ba na iya magana da harshen kamar yadda nake yi da kyau a da.” in ji shi.

“Mutane suna mamaki na tare da yi min biyayya da kuma yi min dariya saboda ni ba Amurke ba ne, kuɗi na da kuma tikitin jirgina na komawa sun danne kasancewa ta bako.”

Matashin da ya kammala karatun digiri ya san shi yana son ya yi aiki kan irin shirye-shiryen da zai zo ya riƙa tallafa wa a matsayinsa na shugaban ƙasa, amma ya sani, kamar sauran matasa, dole ya kasance ya yi abin da zai yiwu a lokacin.

“A mako ɗaya na kasa biyan kuɗin tura takardar neman aiki a gidan waya, a makon da ya biyo baya, kuma dole na rubuta cek na kuɗi na boge domin in yi hayar mawallafin rubutu na tafiraita,” kamar yadda ya rubuta a shekarar 1983.

“Albashi a ƙungiyoyin al’umma sun yi kaɗan wa buƙatun mutum a halin yanzu, saboda haka ina ganin ina fatan samun wani aiki na yau da kullum saboda in tara isassun kuɗin da nake buƙata domin in iya yin irin waɗanan ayyukan ƙungiyoyin al’umma.”

Da ya kama aiki a wani gidan wallafa littattafai, ya ce; “ Ɗaya daga cikin waɗannan matasan waɗanda ake ganin za su ci gaba kuma mutane suka yi ta yaba mini.”

Amman ya yi fargabar cewa aikin babban kamfani ka iya gurbata dabi’unsa kuma ba da jimawa ba ya bar aikin.

Kuma akwai wasu alamu a rubuce-rubucensa da suka nuna irin mutumin da zai iya zamowa daga baya.

A wata wasiƙar da ya rubuta a shekarar 1984 ga Aleɗandra, ya yi tunani a kan abin da zai yi me zai yi da ƙarin ƙarfin faɗa-aji.

“Tunanina ba su kai ƙarfin waɗanda nake da su ba lokacin ina makaranta, amma suna tasiri lokacin da mutum ya dube su,” in ji shi.

 

Exit mobile version