Connect with us

Ka San Jikinka

Garkuwar Jikin Dan Adam (1)

Published

on

Garkuwar Jikin Dan Adam

 

’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zakulo mu ku bayanai game da jikin dan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki.
Allah ta’ala Ya halicci duniya da abinda ke cikinta, Ya halicci jikin dan adam wanda ya ke kewaye da abubuwan cutarwa iri-iri, na zahiri da na badini; amma cikin hikima da baiwa, da tausayi na Sarki mai tsara halitta, sai ya sanya wa dan adam garkuwar jiki domin ta zame ma sa kariya ga barin hadari daga cutuka kala kala.

Abubuwan da su ke ba wa jikin dan adam kariya sun hada da fata, fararen kwayoyin jini, da sauransu.

Kamar yadda na dauki tsawon lokaci ina magana akan jini, rabe rabensa, muhimmancinsa, da ayyukansa a jikin dan adam, bayani na akan fararen kwayoyin halittar jini yana nuna yadda yake bada gudunmawa kan garkuwar jiki. A rubutun baya, na fadi muhimmancinsu da irin rawar da su ke takawa wajen kare dan adam daga farmakin cututtuka a wannan duniya tamu.

Yau idan sarkin ya so, zamu tunkari bayani game da garkuwar jikin dan adam gadan gadan, domin ilimintar daku daga dan takaitaccen ilimin da nake fama da shi. Sabda haka, ku biyo ni.

Kafin na nutsa, akwai bukatar mu tuna cewa, su kwayoyin halittar jini, musamman fararen, an yi su ne domin su taka mhimmiyar rawa wajen bawa jikinmu cikakkiyar garkuwar da ta dace. Duk da cewa wa’adin kwanakin da suke yi a jikin dan adam takaitacce ne. Hakika mun ga bayani game da babbar kwayar halittar (makrofej) mai hadiye cutuka, a turancin likita ana ce  mata “macrophage”. Babban aikinta shi ne hadiye duk wasu bakin halittu ko cutttuka iirn su bakteriya da su ka shiga cikin jikin mutum.

A rubutun baya, munyi duba izuwa takwarar “makrofej” da ake kira da “neutrophil”, wadanda su ma nau’i ne na fararen kwayoyin hallittar jini da su ke zubo da wani ruwan kemikal (wanda karfinsa da kuma sigar aikinsa, kamar ruwam bilich yake: wato parazal ko kuma hypo). Munga yadda su ke kashe kwayoyin cuta su ma. Sai dai akwai wani muhimmin banbanci tsakanin sigar aikin “makrofej” da kuma sigar aikin “nutrofil”.

kwayar halittar makrofej, ta na bin kwayoyin cutar bakteriya ne daya bayan daya, ta na hadiye su amma cikin dan kankanin lokaci matuka; za ta iya hadiye kwayoyin bakteriya sama da guda hamsin a duk sakwan daya! A ɓangare guda kuwa, kwayar halittar nutrofil kamar bam take, mai dauke da sinadaran kemikal masu karfin gaske. Da zarar kwayar nutrofil ta isa gurbin da bakin halittu da cututtuka su ke, sai ta tarwatse, tare da lalata duk wadannan abubuwa masu cutarwa, da ita kanta, a lokaci guda.

To bari muga wata kwayar halittar ta uku da ke bawa jiki garkuwa ko kariya. Wanann kwayar halitta ana ce mata “natural killer cell”, (NK-cells a takaice) ma’ana “kwayar halitta mai dabi’ar kisa”. Ita ma nau’i ce ta farar kwayar halittar jini. Yadda take aiki shi ne—za ta samu bango ko katangar kawayar halittar da cuta ta harba, sai ta huda wannan bango ko katanga. Yin hudar ke da wuya sai ruwan jiki yayi ta shiga cikin farfajiyar wannan kwayar halitta da ta kamu da cuta, haka shi zai jawo ta cika da ruwa ta kumbura daga bisani kuma sai ta fashe. Idan ta fashe, ta mutu kenan, jiki zai samar da wata kwayar halittar lafiyayya ta maye gurbinta.
Za mu iya cewa kwayar “natural killer cell” ‘oga’ ce, saboda aikinta na daban ne; ta na barwa makrofej da nutrofil ragamar kashewa da lankwame kwayoyin cuta. Amma kam duk kwayoyin halittar jiki da suka kamu a sanadiyyar shigar kwayar cuta cikin jiki, aikin “natural killer cell” ne kula da wannan ɓangare.

NK-cells suna da karfi da tasirin gaske wajen fatattakar kwayoyin cutar bairos “virus”da suka kutsa cikin jikin dan adam; kuma suna daya daga cikin tsayayyun dakaru  da jiki ke amfani da su wajen karya lagon cutar “cancer” wato cutar daji.

Hakika wadannan halittu na fararen jini suna iya banbance ‘yan gari daga baki. Ma’ana: su na iya banbance tsakanin kwayoyin halittun jiki daga kwayoyin cutar da su ka shigo cikin jiki. Yayin da wadannan halittu da ke kare jiki su ka kaasa banbance tsakanin ‘yan gari’ da kuma ‘baki’, to fa matsala ta samu, domin za su dinga kaiwa ‘yan gida’, wato asalin kwayoyin halittun jiki farmaki, tare da lalata su. Wannan shi ke haifar da cutar da za mu iya kiranta da ‘kunar bakin waken garkuwar jiki’, a turancinmu kuma “autoimmune disease”.

Yanzu bara mu ga ita garkuwar jiki. Idan ana magana akan garkuwar jiki, akwai muhimman jiga-jigai guda uku da dole sai anyi bayani akansu.  Dabbobi masu kashin baya (ciki hadda mutum, duk da cewa shi mutum ba dabba ba ne, amma an kasafta dashi cikin wannan aji na halittun Allah masu kashin baya), su na kuɓuta ne daga farmaki da hare-hare da su ke fuskanta daga kananan halittu masu cutarwa (microbes) saboda suna da garkuwa. To domin kare kansu, sai Ubangiji Ta’ala ya sanya musu garkuwar domin ta tsaya mu su. Wato kamar dai yadda babban gari ko alkarya ke yi wajen tabbatar da tsaro da kula da kayayyaki da rayukan al’umma, haka shima jikin dan adam ke amfani da garkuwar jiki wajen karewa da kulawa da kuma tsarewa ga barin duk abubuwan da kan kawo nakasu a lafiyar jiki. Kenan za mu iya cewa, jikin dan adam shi ma al’umma ce mai zaman kanta; al’umma ce ta kwayoyin halittu daban daban kamar kwayoyin halittar jini, da na fata, da na kwakwalwa, da na tsoka, da na kashi, da na ‘ya ‘yan rai na maniyyi, da na jijiyoyi, da sauransu. Ga hanyoyin guda uku:

NA FARKO: akwai katangu masu tsayi da karfi da karko da ke kare manyan al’ummatai. Misalin wannan shi ne misalin badala da ta kewaye garuruwan kasashen Hausa. Wadannan katangu na hana mayaka da ‘yan kai hari shiga cikin al’umma. To shima jikin dan adam na da wannan katangu masu bashi kariya. Babbar katangar da ke bashi kariya daga illar cututtuka masu yaki da jiki ta farko ita ce FATA.

Fata ita ce mataki na farko da ke wanzar da garkuwar jiki. Haka kuma, shimfidun tantanin dake kwance cikin sassa da gaɓɓan jiki masu hororo (mucous membranes) su na bada irin ta su garkuwar. (domin sanin yadda fata ke bawa jiki kariya, nemi rubutun da nayi mai taken “Fata A Jikin dan Adam”)

Misalin inda ake samu wadannan shimfidu na tantani sun hadar da: – hanyoyin iska ko numfashi (hanci, makogwaro, akwatun murya, bututun iska da rassansa) da kuma hanyar abinci (baki, bututun abinci, tumbi, karamin hanji, uwar hanji, har zuwa dubura).
NA BIYU: su ne jami’an tsaro masu kai-kawo. A jikin dan adam, halittun da ke gudanar da wannan aiki suna amfani ne da ‘wutar chaji’ ko ince makamashin kuzari da su ke samu daga jiki, shi kuma jiki yake samu daga abinci, da taimakon numfashi domin jiki yaci moriyar amfanin abincin. Bugu da kari, su wadannan jami’ai su na samar da sinadarai na kemikal domin yaki da ‘yan kai hari da mayaka da ‘yan leken asirin jiki’ , kamar dai yadda ba ka rasa jami’an tsaro na zahiri da kayan aiki irinsu kulki, bindiga, ankwa, harsashi da sauransu; to su ma haka jami’an tsaro na jikin dan adam su ke da tsari da shiri na fatatakar makiya. Kaji ikon Allah!

Kash! ‘Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da bayani a kan Garkuwar jikin dan adam.
Advertisement

labarai