An bukaci matakan gwamnati uku na kasar nan, su mayar da hankali kan bunkasa noman rani.
Shugaban Kungiyar Manoman Masara, don samun riba na yankin Arewa Maso Gabas; Alhaji Adamu Muhammad Makarfi ne ya yi wannan kira.
- Dalilin Da Ya Sa Na Dakatar Da Sanusi A Matsayin Gwamnan CBN – Jonathan
- Rahoto Ya Nuna Yadda Noma Ya Samu Koma-baya A Nijeriya
A hirarsa da LEADERSHIP Hausa a Kaduna, Makarfi ya yi nuni da cewa; ya zama wajibi a samar da kyakkyawan tsari, idan kuma ba haka ba; ba mu san irin abin da zai faru a wannan kasa nan gaba ba.
Da yake yin tsokaci kan tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi na dakile ‘yan kasuwar kasar waje zuwa gonakin manoma, don saye amfanin gonar da suka noma kai tsaye; ya ce; wannan tsari abin a yaba ne.
Sai dai, Makarfin ya sanar da cewa; gwamnatin ta makara wajen daukar wannan mataki, domin tuntuni ya kamata a ce an yi wannan tsari.
Har ila yau, a kan kakar noman bana kuwa; Makarfin ya bayyana yadda suka sayi takin zamani da tsada a noman Masarar bana da suka yi.
A cewar tasa, tsadar takin yasa; musamman kanannan manoman Masara Jihar Kaduna, ba su samu damar iya sayen takin ba; ballantana su noma ta.
Ya ce, a bana farashinsa ya ninka; hatta magungunan feshi na kwari ko na kashe Ciyawa da kudin kwadago, dukkaninsu kudaden sun karu.
Ya ci gaba da cewa, haka nan ambaliyar ruwan sama da aka samu a wasu jihohin, kamar Borno, Jigawa da sauransu; hakan ya sake jawo wa wasu manoman yin asara.
Ya kara da cewa, “A matsayina na manomi, bukatarmu ba a sayar da amfanin gona da tsada ba, amma duk da haka; ba za mu so a ce manoma sun yi asara ba, domin asarar manoma; asara ce ga kasa baki-daya”, in ji shi.
Kazalika, ya yi nuni da cewa; duk inda aka ce manomi ya yi noma ya samu faduwa, babban abin da ake jin tsaro; musamman manyan manoma da yawancinsu ke yin noma, don riba; idan suka fadi to fa akwai matsala, domin akasarinsu na ciwo bashi ne a bankuuna; domin yin noman da kuma kudin ruwan da ake dora musu, asarar za ta yi musu yawa.
Shugaban ya ci gaba da cewa, idan manyan manoma ba su yi noma a kasar nan ba, za a samu karancin abinci; hakan ne yasa za ka ga ana yin kira a je a sayo abinci daga kasashen ketare, wanda kuma idan aka yi hakan; ko shakka babu Nijeriya za ta iya yin asara mai yawa, wanda ka iya durkusar da tattalin arzikinta.
A karshe, ya bayyana cewa; idan har za a sayo Masara a kasar waje ba tare da an noma a cikin gida ba, akalla za a iya yin asarar kimanin Naira tirilyan goma; inda ya yi nuni da cewa, idan ba a bai wa manoman kasar nan taimakon da ya dace ba; karamar matsala ce za ta iya zama babba.