“Gazawar el-Rufai Ta Ceto Dalibai Na Jefa Shakku A Zukatan Al’ummar Kaduna”    

Daga Abubakar Abba Kaduna

Gazawar gwamnatin jihar Kaduna wajen ceto daliban Kwalijin Afaka da na Jami’ar Greenfield a yanzu kuma a cikin gaggawa, na kara jefa shakku a zukatan al’ummar jihar Kaduna da zubar da kimar gwamnatin jihar.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin  sanarwar da kungiyar yaki da annobar Korona reshen jihar Kaduna (ASCAB) da kuma ta kare rajin ‘yancin ‘yan Adam suka   fitar a kaduna,  inda kuma suka  koka kan yadda ‘yan bindiga ke yawan kai hare -hare a karkara  da kuma a cikin birane  a ‘yan kwanukan nan a jihar  Kaduna.

Koken wanda Kwamarade Aliyu Attahiru jami’in rikon kwarya na kungiyar (ASCAB) da kuma takwaransa na  kwamitin kare rajin ‘yancin ‘yan Adam Manasse Turaki  suka sanya wa hannu sun  yi nuni da cewa hakan abin damu wa ne matuka, inda ta kara da cewa,  jama’a a gidajen su da kuma a cikin al’umma,  ba su tsira ba kuma su na ci gaba da zama a cikin jin tsoro da fargaba.

A cewar sanarwar, hakan ya kuma nuna cewa, alummar sun fara fidda tsammani kan da amincewa kan karfin gwamnati na cika alkawuranta  da ke a cikin  kundin tsarin mulkin kasar nan  na kare lafiyarsu da ta dukiyoyinsu a zamansu na ‘yan jihar.

Sanarwar kungiyar mai taken ‘ Matsayin Mu Kar A Bar daliban Mu Su Mutu a Hannun ‘Yan Bindiga’, kungiyar ta yi muni da cewa,  ganin yadda a yanzu, masu garkuwar  suka fito da sabon  salon sace marasa karfi,  musamman  a  makarantun boko domin neman kudin fansa mai tsoka a cikin gaggawa, “Muna kira ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed Nasir  el-Rufai,  da ya sauke  nauyin da ke a kansa, na kare lafiya da kuma dukiyoyinsu ‘yan jihar  a yanzu kuma a cikin gaggawa don ceto daliban Jami’ar  Greenfield da na Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya  da ke Afaka a cikin jihar.”
A cewar sanarwar, “Muna son mu tunatar da Nasiru el-Rufai kan rantsuwar da ka yi ta kare al’ummar jihar wacce hakan ne aikin sa na farko, musamman domin a ceto sauran daliban  jami’ar Greenfield,  musamman ganin yadda ‘yan bindigar suka yi ikirarin hallaka su idan ba a biya su kudin fansa ba”.

A karshen, sanarwar ta koka kan yadda jami’an tsaro a jihar suka Gaza yin wani katabus ko yin hanzari wajen daukar dabarun gano inda masu garkuwar da daliban suke.

Exit mobile version