Gbajabiamila Ya Zargi Jihohi Kan Tabbatar Da ‘Yancin Kananan Hukumomi

Gbajabiamila

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Shugaban majalisar wakilai, Honarabul Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa, ya kamata a dora wa majalisun dokoki na jihohi alhakin jinkirin tabbatar da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi a Nijeriya.
Gbajabiamila ya bayyana yadda Majalisar dokoki ta zartar da kudirin bayar da ikon cin gashin kai ga kananan hukumomi, amma shawarar ba ta samu amincewar kashi biyu bisa uku na jihohi ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, a wani taron horon shugabanci wanda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Honarabul Ndudi Elumelu, ya shirya wa shugabannin kananan hukumomi da kansiloli daga Jihar Delta.
An tambayi Gbajabiamila abin da majalisar tarayya ke yi don ceto matakin na uku na gwamnati ga barin rugujewa, sai ya ba da amsa da cewa, “Ba namu ba ne a matsayinmu na ‘yan majalisa, yin hakan. Na tabbata kun yi mamaki, amma a zahiri mutane su tashi tsaye ne, dalili kuwa shi ne muna da gyaran tsarin mulki, za mu jefa shi ga mutane kuma za su yanke shawara.”
“Mun yi hakan a karo na karshe amma mun koma jihohi kuma ba mu iya samun kashi biyu cikin uku ba. Akwai tsari, kuma mun bi tsari. Mun yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima a karo na karshe, amma kashi biyu bisa uku na jihohin ba su yarda da mu ba. Don haka, mutane ne za su yanke shawara ko suna son cin gashin kansu ko ba sa so. Za mu yi abin da ya kamata mu yi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.”
Kakakin majalisar ya bayyana yardarsa na cewa, a karshen horon, jami’an majalisar za su sami ilimi mai yawa kan abin da jagoranci yake nufi.
“Wadansu mutane an haife su ne da jinin shugabanci, wasu suna koyon neman jagoranci amma ta kowace hanya, ko an haife ka jagora ko ka same shi, dole ne ka je wannan horon don ka sami damar amfani da gogewar ka da halayen ka don habaka kwarewar ka.

Exit mobile version