Yusuf Shuaibu" />

Gobara Ta Lakume Dukiyar Miliyoyin Kudi A Kasuwar Jihar Oyo

A cikin wannan makon ne, gobara ta lakume dukiyar miliyoyin nairori a wata kasuwa da a ke kira da suna Orita-Aperin, da ke cikin garin Ibadan babbar birnin Jihar. Har zuwa lokacin da a ke hada wannan rahoto, ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Da ya ke bayani a kan lamarin, shugaban ‘yan kasuwar Orita-Aperin, Mista Abiodun Ahmed, ya bayyana cewa, an yi asarar dukiyar miliyoyin Nairori a kasuwar. Ya kara da cewa, har yanzu ba a san musabbabin tashin wutar ba.

Ya ce, “Wutar ta tashi ne da misalin karfe 12 na daren ranar Juma’a, nan ta ke mu ka sanar da hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo, amma abin takaici shi ne, lokacin da su ka isa wurin, sai motarsu ta ki yin aiki, mun yi kokarin kashe wutar da kai mu, idan da ba mu yi hakan ba, to sai asarar tafi wanda a ka yi a yanzu.”   

Ahmed ya ce, mafi yawancin shagonan da gobarar ta lakume, ba su dade da sayo kayayyaki ba, ya kara da cewa, wannan shi ya sa lamarin ya yi kamari. “Shagonan ya gobarar ta shafa sun hada da, shagunan sayar da gwalagwalai, shagunan sayar da kayan abinci, shagunan sayar da man-ja, shagunan sayar da magunguna da dai sauran su, akwai tsabar kudi na naira miliyan biyar da dubu dari shida a wani shagon sayar da gwal lokacin da wutar ta tashi, da yawa daga cikin kayayyakin da su ka kone a shagon sayar da magunguna ba za a iya samun su ba, domin ba a sayar da su a kasuwa,” in ji shi.    

Ahmed ya cigaba da cewa, ya bukaci gwamnatin Jihar Oyo ta taimaka wa ‘yan kasuwan wadanda su ka tafka asara a wannan gobara.

Wata ‘yar kasuwa wacce shagonta ya kone kurmus mai suna Latifa Adegbola, ta roki gwamnatin Jihar Oyo da ta taimaka wa ‘yan kasuwar da su ka tafka asara da kudade, saboda ‘yan kasuwan su na amsar kayayyaki bashi ne, sai idan sun sayar da su bayar da kudi. “Wuta ta kone duka kayayyakin shagona kurmus, saboda haka, mu na kira ga gwamnatin Jihar Oyo ta taimake mu, domin mu cigaba da gudanar da kasuwancinmu yadda ya kamata.”

Wata mai sayar da tattasai da albasa, Mariam Oladepo, ta bayyana cewa, ta yi asarar kayayyaki wadanda su ka kai na naira dubu dari a wannan gobarar. Ta kara da cewa, shagonata ya kone kurmus babu abinda ya rage, hatta abinda yaranta za su ci, a yanzu ba ta da shi.

Exit mobile version