Wata gobara da ta tashi cikin dare ta kashe iyalin wani mutum su biyar a unguwar Kofar Sauri da ke cikin birnin Katsina.
Gobarar, wadda ta tashi da safiyar ranar Litinin, ta ƙone gidan ƙurmus kafin maƙwabtansu samu damar taimaka musu.
- Gwamna Adeleke Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
- Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Haƙar Ma’adinai Na Tsawon Watanni 6
Waɗanda suka rasu sun haɗa da uba, uwa da ’ya’yansu uku, kuma sun maƙale a cikin gidan ne yayin da wutar ta bazu ko ina.
ADVERTISEMENT
Wasu mazauna yankin sun ce gobarar na iya samo asali ne daga wutar lantarki da aka kawo.
Wasu kuma sun danganta bazuwar gobarar da iska mai ƙarfi.
Har yanzu ’yansanda da hukumomin kashe gobara na jihar da na tarayya ba su fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.














