Jama,a barkammu da juma,a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma,a. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa. A you ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan anyi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a tare da kaiziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka
Sako daga Fati Tijjani:
Assalaikum alaikum!
Al’umar musulmi baki daya, ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na mamana da babana ina musu fatan alkhairi da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana kannena da fatan sunyi sallar juma’a lafiya. Ina gaida kannan mamana da kannan babana tare da yi musu fatan anyi sallar juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da juma’a.
Sako daga Habu Yallabai, Katsina
A wannan rana ta Juma’a, ina mika sakon gaisuwata ga mahaifita da mahaifina da kuma matata, da fatan dukkaninsu za su kasance cikin koshin lafiya.
Haka nan, ina so na yi amfani da wannan dama; na sake mika gaisuwata ga ‘yan’uwana baki-daya da kuma abokaina, musamman abokanan aikina a daidai wannan lokaci.
Cikin abokanan aikin nawa akwai, Mu’azu, Shamsu, Jamilu, Henry, Joy, Halima, Saratu da Habibu.
Haka zalika, ba zan manta ‘ya’yana ba; Abdul, Fatima da Ahmad. Sai kuma kannena, Ibrahim, Adnan, Aliyu, Sadiya, Umma da kuma Fa’iza.
Sako daga Habib Idris
Assalamu alaikum da fatan mun wayi gari cikin koshin lafiya na safiyar Jumma’a babbar rana Allah ya bamu lada da albarkacin dake cikin ta, ya kawo mana sauki a halin rayuwar da muke fuskanta
Ina mika sakon gaisuwa ta Iyayena Malaman makaranta ta na Boko Da Islamiyya musamman ma Unty Salaha da Malam Ishak,da sauran dukkan Malamaina.
Abokaina da suka hada da Adamu N. Muhammad, Abdulsalam Umar, Ashiru Muktari, Kamal Aliyu,Mubarak Yusuf, Imam Idris, da kuma kanuwata Nana Hauwa’u Idris Aliyu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp