Jama’a barkanku da wannan rana ta juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da yake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa, har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana, inda sakon farko ya fara da cewa;
- NLC Ta Baiwa Gwamnati Kwanaki 7 Don Magance Badaƙalar Satar Kuɗin Ma’aikata
- Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe
Sako Daga Hassan Baros Yalleman
Ina mika sakon gaisuwata ga maigirma Honarabul Makki Abubakar yalleman, da Yayana Salihu Gaji Yalleman, da Pamasit Hashim Ubali Yusuf, dafatan sunyi juma’a lafiya.
Sako daga Mansura Muhammad Garko
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga Mahaifana, da ‘yan’uwana Fatima Muhammad, Sadiya Muhd, Tahir Muhammad, sai kawayena na tsohuwar makarantarmu da na unguwarmu kamai Zainab Abdulkadir, Shamsiyya Muhammad, Marakisiyya Shu’aib, da fatan sun yi Juma’a lafiyya.
Saki daga Kassim Bello Muhammad Makarfi daga Jihar Kaduna
Ina yi wa ‘yan’uwa musulmi na fadin duniya fatan alheri, da ilahirin ahalina na kusa da na nesa kamar su Amir Saleh, Amina Bello Makarfi, Sa’adatu Muhammad Kanwa, Kamal Sagir Garba, da dai sauransu. Da fatan sun yi juma’a lafiyya, Amin.
Halima Galadima Bebeji daga jihar Kano
Idna gaishe da Mahaifiyata Hajiyya Zahra’u Mamman, da mahaifina Alhaji Muhammad Galadima Babeji. Sai sakon gaisuwata zuwa ga al’ummar ‘DYZ Group’ kamar su Khadijah Ibrahim Umar Jambulo(Deeja J), Jamila Kabir Hassan(Miss Jamcy), Zakiyya Murtala Ajingi da dai sauran wadanda ban amabato ba, da fatan sun yi juma’a lafiyya.
Sako daga Munir Shamsudden Hadejia daga jihar Jigawa
Ina gaida ‘yan babban gidanmu irinsu Honarable Alhaji Aliyu Bukar Maigatari, Mallam Yunusa DanLadi Birniwa, Hajiya Hafsatu, sai matata Zaliha, da fatan sun yi
juma’a lafiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp