Marigayi Sarkin Koko na biyar Malam Muhammad Bello, ya rasu ne a ranar juma’a 21 ga watan Yuli na shekarar 2023. Shi ne babban dan Sarkin Koko Salihu Marigayi, Sarki na biyu ga tarihin kafa garin Koko dan Malam Musa dan Malam Muhammadu Dangindi wanda shi ne Sarkin Koko na farko daga shekarar 1907 zuwa 1944.
An haifi Marigayi Sarkin Koko, a cikin garin Birnin Kebbi a shekarar 1936. Ya fara karatun addinin Musulunci a Koko. Daga haka kuma ya sami ilimin elemantare a cikin Koko a shekarar 1943. Amma a shekarar 1948 ya halarci Makarantar Midil da ke Sakkwato, inda ya hadu da abokan karatu kamar su: Alhaji Idirisu Koko (Madawaki) da Alhaji Attahiru Sarkin Kudun Gwandu da Sarkin Sudan Shehu Malami da Alhaji A. A. Dogondaji da Marigayi Malami Minista da Alhassan Yauri da dai Sauransu.
- Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Amsa Tambaya Game Da Taron Ministocin Muhalli Da Yanayi Na G20
- Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Amsa Tambaya Game Da Taron Ministocin Muhalli Da Yanayi Na G20
Haka Kuma a cikin shekarar 1953, ya sami nasarar cin jarabawar ta midil inda ya zarce zuwa H.T.T.C Ilorin a shekarar 1954. A cikin wannan shekarar ne aka fara yin karatun Grade II, ba tare da an yi Grade III da Grade IB ba, a duk Arewacin Nijeriya, an fara karatu ne a Toro da kuma Makarantar horon Malami ta Katsina.
Har ila yau, Marigayi Sarkin Koko, Malam Muhammadu Bello ya kammala karatunsa na fannin koyarwa a Ilori cikin shekarar 1957, inda ya sami takardar shaidar malanta mai daraja ta biyu, wato (Grade II) da kyakkyawan sakamako, wanda ya ba shi wani lakabi da ake ce masa “Haifaffen Malami” (A Born Teacher), wannan suna ne da malamansa suka lakaba masa domin basirar da Allah ya hore masa. Inda har lambar yabo ya samu a lokacin bikin al’adu na “Northern Festibal of Arts, Kaduna” a shekarar 1955.
Kazalika, Marigayi Sarkin Koko Malam Muhammadu Bello ya fara aiki da Gwandu ‘Natibe Authority’ a matsayin Malami a garin Birnin Kebbi, wato a Makarantar Midil. A wannan lokaci ya rike mukamai kamar, (House Master) da (Games Master), wanda a karkashin jagorancinsa dalibansa suka ciyo kofin da Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello ya a sa shekarar 1960.
Lokacin da Malam Bello ya kama aiki a Makarantar Midil ta Birnin Kebbi, babu shakka ya tarar da akwai tabarbarewar ilimi, har ta kai yana da matukar wahala dalibi ya samu cin jarabawar (Common Entrance).
Daga nan, a wannan lokacin ne aka ba shi ‘yan aji biyar har zuwa aji bakwai, kuma cikin ikon Allah kusan kowannensu ya sami nasarar cin jarabawarsa kamar yadda ake bukata. Kuma Marigayi Sarkin na alfahari da wadannan dalibai nasa.
Daga hakan sai ya zama Shugaban wata Makaranta a farko a cikin Birnin Kebbi, wato (Day Senior Secondary School) a wannan lokaci duka dalibansa ‘yan aji bakwai sun ci jarabawarsu suka wuce zuwa wasu Makarantau na gaba.
A shekarar 1963 Marigayi Sarkin Koko ya zarce zuwa ” Adbance Teacher College Zaria”, inda ya sami yin kwas na N.C.E., kuma yana daya daga cikin daliban farko a fadin tarayyar Nijeriya da suka fara wannan kwas din. Bayan ya kammala wannan karatu a cikin shekarar 1965, ya dawo Makarantar Sakandare ta Birnin Kebbi, inda ya koyar da ‘yan aji biyar (form 5). Har ilayau kasancewar Sarkin masani a fannin koyarwa, sai ya yanke shawarar komawa gida Koko a matsayin Shugaban Makarantar firamare da ake kira ” Salihu Primary School” domin tallafa wa ci gaban ilimin yankinsa, kuma a zamaninsa an samugaggarumar nasara, wato a shekarar 1966. Dalibansa sun zama wasu abin ayi alfahari da su ciki da wajen Jihar Sakkwato da Kebbi da Zamfara.
Saboda kula da sha’awar ilimi ya zarce zuwa Jami’ar A.B.U. Zaria, inda ya karanci (Educational Administration), nan ma ya kammala cikin nasara tare da samun kyakkyawan sakamako, ya kuma sami yabo daga kwamishinan Ilimi na Arewa maso Kudu, a wannan lokacin.
Haka Kuma a shekarar 1967, an zabi Marigayin a matsayin dan kasar Gwandu na farko da ya rike mukamin (Education Officer), a hukumar ilimi ta kasar Gwandu. Har ilayau a shekarar 1969, ya je jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya yi karatu a fannin (Administratibe Management).
Bayan haka kuma ya yi kwas a fannin (Leadership and Citizenship), a Jos shere Hills da Awka da Awgu. Daga nan kuma an aika shi bangarori da ake yaki, a wancan lokacin domin yin wasu ayukkan a can cikin kasar Ibo, bayan ya kammala wannan aiki ne ya dawo gida da mukamin “District Officer” (D. O), wato na Jihar Sakkwato.
Kazalika, a shekarar 1973, an kai shi ma’aikatar gona da ma’adinai inda ya yi aiki tare da kwamishina Tanko da Marigayi Alhaji Wazirin Gwandu. Sai kuma a shekarar 1975, an kai shi Ma’aikatar (Ministry of Animal Health and Forest Resources), a karkashin kwamishina Wazirin Gwandu da mukamin (Touring Officer). A shekarar 1976, ya zama sakatare na farko a ‘Ministry of Trade and Industries” mai kula da biyam kudade.
Marigayin Sarkin Koko, ya sami mukamin manaja a ma’aikatar samar da bruwa na Jihar Sokoto daga nan kuma ya yi aiki ‘Ministry of Water and Electricity’ a matsayin (Principal Assistant Secretary). Haka kuma a shekarar 1983 sai jama’ar Koko suka bukaci ya yi ritaya domin ya shigo fagen siyasa, a wannan lokaci ne aka zabe shi a matsayin Dan Majalisar dokokin jiha a shekarar 1983.
Daga nan bayan juyin mulkin da aka yi a cikin wannan shekara ta 1983, sai marigayin ya koma ga aikinsa na koyarwa a shekarar 1984, inda ya ci gaba da aiki da ‘Birnin Kebbi Polytechnic’. A shekarar 1985 ya zama Director a (F.A.S.C.O) Sokoto. A cikin shekarar 1988 ya zama shugaban Hukumar wasan motsa jiki na jihar Kebbi “State Athletics”. Daga nan Malam Muhammadu Bello Koko ya zama mamba na dindin a hukumar malamai ta jihar Kebbi ‘Permanent Member Teachers Serbice Board’ Kebbi statei.
Daga nan, a shekarar 1997- 1999 an ba shi Sarautar Sarkin Sudan Uban Kasar Lani. Daga nan kuma ya samu nasarar zama Sarkin Koko na biyar a shekarar 2020 zuwa 2023.
Yana da mata daya da ‘ya’ya 15 da jikoki masu yawa da ma ‘ya’yan jikoki masu yawa. Babban abin da marigayin yake sha’awa shi ne karatu. Daga cikin ‘ya’yan marigayin akwai Shugaban Hukumar Kula da Tashoshi Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA), Muhammad Bello Koko, akwai tsohon babban ma’aikacin Banki, Alhaji Shehu Muhammad Bello Koko wanda ya yi takarar kujerar dan majalisar wakilai a mazabun Maiyama/ Koko Besse wanda a halin yanzu suna a kotun sauraren kararakin zabe da ke zaman ta a Birnin Kebbi, jama’a da dama sun yi tattaki zuwa garin koko domin gaisuwar ta’aziya ga iyalan marigayin.
Haka kuma manyan Ma’aikatan Gwamnatin na tarayya da na jihohin kasar nan har ma da wajen kasar sun zo garin na Koko kan rasuwar Sarkin na Koko, Gwamnoni, wakilan wasu Sarakunan na kasar nan da Sauransu duk sun zo don ta’aziya rasuwar Sarkin Koko. Allah ya jikansa da rahama.