• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gundogan Ya Amince Ya Sake Komawa Manchester City 

by Rabilu Sanusi Bena and Sulaiman
1 year ago
in Wasanni
0
Gundogan Ya Amince Ya Sake Komawa Manchester City 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Manchester City da Ilkay Gundogan sun cimma cikakkiyar yarjejeniya akan komawa kungiyar ta kasar Ingila domin ci gaba da taka leda.

Gundogan, mai shekaru 33, zai rattaba hannu kan kwantiragin shekara daya da City, tare da zabin karin watanni 12.

  • Mutane 4 Sun Mutu, 6 Sun Bace Sakamakon Kifewar Kwale-kwale A Kano
  • Mun Gano Hanyoyin Da Ake Satar Man Fetur A Nijeriya – NNPC

Dan wasan zai bar Barcelona a kyauta, shekara guda bayan ya koma kungiyar a watan Yunin 2023.

Labarai Masu Nasaba

Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City

Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface

Gundogan ya koma Barcelona a bazarar da ta wuce, inda ya buga wasa 36 a kakar wasa ta farko, amma an gaya masa cewa, baya cikin jerin ‘yan wasan da sabon kocin kungiyar, Hansi Flick zai tafi da su bayan ya maye gurbin Xavi a farkon wannan bazarar.

City ta kasance kan gaba don tabbatar da dawowar Gundogan, inda dan wasan tsakiyar ya tattauna da Pep Guardiola kan yiwuwar komawa Manchester kuma kocin ya ba shi dama.

A baya Gundogan ya buga wasanni 188 a karon farko a City, inda ya lashe kofin Premier sau biyar, kofunan FA guda biyu da kuma gasar zakarun Turai sau daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kaddamar Da Shirin The Bond Karo Na Biyar A Kasar Masar

Next Post

An Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Wani Artabu Da Sojoji A Filato

Related

Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City
Wasanni

Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City

1 day ago
Boniface
Wasanni

Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface

3 days ago
Ronaldo Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Hong Kong
Wasanni

Ronaldo Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Hong Kong

4 days ago
Yadda Arsenal Ta Doke Manchester United Da Ci 1-0
Wasanni

Yadda Arsenal Ta Doke Manchester United Da Ci 1-0

6 days ago
Waye Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
Wasanni

Waye Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?

7 days ago
Me Ya Sa Ciwon ACL Ya Zama Barazana Ga ‘Yan Wasan Kwallo?
Wasanni

Me Ya Sa Ciwon ACL Ya Zama Barazana Ga ‘Yan Wasan Kwallo?

7 days ago
Next Post
Sojoji

An Kashe 'Yan Bindiga Da Dama A Wani Artabu Da Sojoji A Filato

LABARAI MASU NASABA

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

August 23, 2025
Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari

Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari

August 23, 2025
CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

August 23, 2025
Yadda Ake Alale

Yadda Ake Alale

August 23, 2025
Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

August 23, 2025
Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata

Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata

August 23, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Gangamin Tattara Fina-Finai Da Talabijin Da Aka Samar Bisa AI A Los Angeles

CMG Ya Kaddamar Da Gangamin Tattara Fina-Finai Da Talabijin Da Aka Samar Bisa AI A Los Angeles

August 23, 2025
Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

August 23, 2025
Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

August 23, 2025
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.