Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya naɗa matasa sama da 200 a matsayin hadimansa.
Za su yi aiki a matsayin masu ɗaukar rahoto, manyan mashawarta na musamman, da kuma mataimakan fasaha a ɓangaren yaɗa labarai da sadarwa.
- Rashin Haɗin Kai Na Barazana Ga Makomar Arewa – Sarkin Zazzau
- Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 6 A Nasarawa
Gwamna Buni ya ce wannan mataki yana da nufin bai wa matasa dama su shiga cikin harkokin mulki tare da amfani da sababbin dabarunsu don inganta sadarwar gwamnati.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, Mallam Yusuf Ali, Babban Mataimaki na Musamman kan Sadarwa da Tsare-tsare, ya ce wannan naɗin yana nuna yadda gwamnan ke ƙoƙarin bai wa matasa dama su taka rawa wajen ci gaban Jihar Yobe.
Ya ƙara da cewa wannan mataki yana tabbatar da irin salon shugabancin Gwamna Buni wanda ke mayar da hankali kan haɗin kai, ƙirƙire-ƙirƙire, da bunƙasa ƙwarewar jama’a.
Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar.
Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp