A ranar Juma’a ne gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kai ziyara gidan gyara hali da ke Gusau, inda ya sanya aka saki ɗaurarru 31, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi dama.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa, gwamnan Dauda ya yanke shawarar yin haka ne bisa natsattsen binciken da aka gudanar game da waɗannan masu zaman wakafin.
- Kungiyar Masu Masana’antu Sun Yi Hasashen Matsala Ga Sashen
- Babban Layin Samar Da Wutar Lantarkin Nijeriya Ya Lalace Sau 7 A 2024
Sanarwar ta ƙara da cewa, tsarin mulki ya ba gwamnoni damar sassauta zaman yari ko ma yafiya ga wadanda ke zaman gidan yari.
Cikin jawabin da ya gabatar a wurin sanya hannu a wannan yafiya, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ɗaurarru ne masu laifuka daban-daban aka yafe musu domin a ƙarfafa musu gwiwa su zama ‘yan ƙasa nagari masu bin doka da oda.
“A yau na aiwatar da ikon da kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, sashe na 212(1) ya ba ni, wanda ke da nufin yaye duk wani ƙunci da damuwa ga masu zaman gidan yari.
“An yanke wannan shawara ne bayan zurfafa binciken da aka yi game da waɗannan ɗaurarru, wanda kuma ya tabbatar da da-na-saninsu bisa abinda suka aikata a baya.
“Bugu da ƙari, na amince a bai wa kowanne daga cikinsu Naira 50,000 don su samu abin dogaro da kai bayan fitar su cikin jama’a.
“Wannan yana daga cikin ƙoƙarin gwamnati na na rage cunkoso a gidajen yari, musamman a wannan lokacin da muke yawan kamo ‘yan bindiga da masu ba su bayanan sirri.” In ji Gwamna Dauda
Bayan zagaya cikin gidan yarin, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin bayar da taimakon da ya wajaba ga gidan yarin da ke Gusau.
Tun farko a nasa jawabin, shugaban Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar Zamfara, Dr. Umar Galadima, ya jinjina wa Gwamna Lawal bisa ziyarar da ya kai, tare da yafe wa ɗaurarrun.