Daga Mustapha Abdullahi,
Gwamnan Jihar Borno, Banagana Umara Zullum ya kai ziyara Hukumar raba-daidai ta kasa, inda ya bukaci Hukumar ta bayar da muhimmanci ga ‘yan asalin Jiharsa wajen daukar aiki.
Gwamna Zullum lokacin da ya kai ziyarar a ranar Litinin, nan take ya bukaci hukumar da ta bayar da muhimmanci ga Jiharsa a duk lokacin da za a dauki aiki a Nijeriya.
Zullum, ya samu gagarumar tarba daga shugaban hukumar da kuma Sakataren hukumar, Dokta Muheeba F. Dankaka da Mohammed Bello Tukur.
Da ta ke mayar da jawabi, Shugabar Hukumar Dokta Muheeba F. Dankaka ta yi alkawarin duba wannan bukata da Gwamna Zulum ya gabatar, inda ta tabbatar da cewa halin da Jihar Borno ke ciki abu ne sananne ga kowa, don haka za a yi wa Jihar Borno adalci a wajen rabon guraben aikin da za a samar.
Shugabar hukumar wacce ta ke tare da daukacin Kwamishinoninta da ke wakiltar Jihohin Nijeriya, duk sun gode wa Gwamna Zulum bisa irin kokarin da yake yi domin ganin rayuwar jama’a ta inganta a kodayaushe.
Wadanda suke a cikin tawagar Gwamnan, sun hada da shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Farfesa Isa Hussaini Marte, da wasu daga cikin Kwamishinoni, da kuma wasu al’ummar Jihar Borno.