Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya yi Allah-wadai da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan Banga a dajin Mansur da ke Duguri/Gwana a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
‘Yan Bangar waɗanda ke kan aikin sintiri a yankin dajin Dmzuguri, Mansur, da Dajin Mada, sun gamu da kwantan-ɓaunar ‘yan bindiga ne inda suka kashe kusan ‘yan Banga 10 a ranar Lahadi.
- Xi Da Shugaban Majalisar Turai Da Shugabar Kwamitin EU Sun Tayawa Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Hulda
- Zulum Ya Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 6,000 Garuruwansu A Borno
Gwamna Muhammad ya bayyana harin a matsayin abin takaici, inda ya ce, ya zama abin zaburaswa kan barazanar da masu aikata laifuka ke yunƙurin janyo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma wanda a cewarsa ba zai bar hakan ya faru ba.
A sanarwar da kakakinsa Mukhtar Gidado ya fitar, gwamnan ya miƙa saƙon jajantawa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, al’umman ƙaramar hukumar Alkaleri da ma mutanen jihar Bauchi baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan jaruman da suka rasa rayukansu a ƙoƙarinsu na kare yankunansu.
Gwamnan sai jaddada aniyar Gwamnatinsa na daƙile kowace irin nau’in barazanar tsaro a dukkanin faɗin jihar.
Ya yi kira ga jama’a da su rika zama cikin haɗin kai da bayar da gudunmawarsu ga jami’an tsaro tare da samar musu da bayanan sirri a kan lokaci da zai bada damar daƙilewa ko magance matsalolin tsaro a kan lokaci.
Yayin da ya ke tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tana kan aikin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro wajen ganin an cafko waɗanda suka aikata wannan kisan domin su fuskanci Shari’a, Gwamnan ya kuma bada tabbacin cewa zai yi ko menene domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyar jama’an jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp