Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi marayu 95 daga gidan marayu na jihar, tare da yin alƙawarin ba su cikakkiyar kulawa a fannin walwala, da ilimi, da lafiyarsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata liyafar murnar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Gwamna Yusuf, ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi alƙawarin bayar da cikakkiyar kulawa ga marayun, yana tabbatar da cewa dukkan buƙatunsu, ciki har da ilimi daga matakin firamare zuwa jami’a, da kula da lafiya, da abinci, za su kasance ƙarƙashin kulawar gwamnatinsa a tsawon wa’adin mulkinsa.
- Gwamnan Kano Ya Nada Hauwa Isah Ibrahim Manajan Daraktan ARTV
- Ranar ‘Yanci: Jihar Kano Ta Zama Madubin Dubawa A Kan Kyakkyawan Shugabanci – Gwamna Abba
Ya yi alƙawarin ɗaukar yaran kamar nasa, tare da ba su damar cimma burinsu, yayin da ya kuma bada gudummawar kayan abinci da suka kai miliyoyin Naira domin tallafa musu.
“Kun zama ‘ya’yana yanzu, zan kula da ku kamar yadda nake kula da nawa,” in ji gwamnan yayin da ya ke tabbatar wa marayun.