Mallam Umar Namadi, Gwamnan Jihar Jigawa, ya samu lambar yabo ta LEADERSHIP ta Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2024, saboda irin kyakkyawan jagorancinsa wanda ya haÉ—a da gudanar da mulki mai cike da gaskiya da riÆ™on amana da samar da ababen more rayuwa da inganta tattalin arziÆ™i da kuma tallafawa jama’arsa a É“angarori da dama na rayuwa.
Samun wannan yabo ya nuna yadda jagorancinsa ya haifar da sakamako da ci gaba mai ɗorewa wajen inganta rayuwar al’ummarsa.
- Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati 2024: Shugaban Kwastam, Alh. Bashir Adewale Adeniyi
- Gwarzon ÆŠan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters
Tarihi Da Karatunsa
An haifi Umar Namadi a garin Kafin-Hausa da ke jihar Jigawa, Allah ya albarkaci gidan da ya fito da ilimin addini. Kakansa shi ne Babban Limamin Kafin-Hausa, wanda ya kafa harsashin kyakkyawan jagoranci da sadaukarwa a rayuwarsa. Namadi ya fara karatunsa na firamare a Kafin-Hausa Central Primary School, sannan ya ci gaba a Mallam Madori Teachers’ College, inda ya samu takardar Teachers Grade II Certificate a shekarar 1982.
Bayan haka, Namadi ya rubuta jarrabawar A-Level a 1984, nasarorin da ya samu a fannin ilimi sun ba shi damar shiga Jami’ar Bayero ta Kano, inda ya kammala digiri a ɓangaren Akanta a 1987. Daga baya ya sake samun digiri na biyu a fannin Tsare-tsaren Kasuwanci (Business Administration) (MBA). Kazalika, Namadi mamba ne na ƙungiyoyin ƙwararru Akantoci da suka haɗa da; Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN), da Nigerian Institute of Management, da kuma Chartered Institute of Taxation.
Ƙwarewa a Fannin Kuɗi da Kasuwanci
Namadi ya yi aiki a fannonin kuÉ—i da masana’antu, inda ya fara aikinsa a matsayin babban jami’i mai kula da Æ™ananan bankuna (Principal Inspection Officer a National Board for Community Banks). Daga nan, ya yi aiki a Kaduna Textiles Limited da kuma rukunin kamfanonin Dangote, inda ya riÆ™e matsayi daban-daban, har ya zama jami’i mai kula da kuÉ—i (Financial Controller na Dangote Sugar Refinery) da sauran sassa na rukunin kamfanin Dangote.
Bayan haka, Namadi ya shiga harkokin kasuwanci na kansa, inda ya kafa kamfanonin ÆŠanmoÉ—i Foods Processing Limited da Danmodi Farms Limited. Danmodi Foods ya zama masana’antar sarrafa shinkafa ta farko mai zaman kanta a Jihar Jigawa, wanda ya samar da ayyukan yi da dama ga matasa da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shigarsa Siyasa
Namadi ya fara siyasa ne a shekarar 2015 lokacin da ya zama kwamishinan harkokin kuÉ—i da tsare-tsare na Jihar Jigawa. A wannan matsayi, ya kawo sauye-sauye masu muhimmanci kamar aiwatar da tsarin asusun bai É—aya (Treasury Single Account (TSA), wanda ya tabbatar da gaskiya da inganci a sarrafa kuÉ—aÉ—en jihar. Hakanan, shi ne ya fara tsara takardun kuÉ—aÉ—en jihar daga cikin gida, ba tare da dogaro da kamfanoni na waje ba.
Daga 2019 zuwa 2023, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, inda ya kasance ginshiƙi kuma abin koyi wajen riƙon gaskiya da amana. Wannan ya tabbatar da karɓuwarsa da amincewar jama’a har aka zaɓe shi a matsayin gwamna a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Jagoranci a Matsayin Gwamna
A matsayinsa na gwamna, Namadi yana jagorantar jihar bisa hangen nesa, inda ya fi mayar da hankali kan ayyukan more rayuwa da walwalar ma’aikata da noma da ilimi. Gwamna Namadi ya gina hanyoyi da gadoji da dama a faɗin jihar don haɗa yankunan karkara da birane. Wannan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙi da rage cunkoso a wuraren kasuwanci.
Noma: Ya tallafa wa manoma ta hanyar samar da taki mai rahusa da kayan aikin gona da bayar da horo kan sababbin fasahohin noma. Wannan ya ƙara samar da abinci da ayyukan yi ga matasa a jihar.
Ilimi: Namadi ya tabbatar da gyaran makarantu da ɗaukar malamai don inganta tsarin karatu. Hakanan ya kafa Gidauniyar tallafawa ilimi (Educational Foundation) tare da ƙanin sa, Dr Abdullahi Namadi, don tallafa wa ilimin yara.
Tallafi ga Jama’a
Namadi ya kasance gwarzo wajen tallafawa matasa da mata ta hanyoyin samar da jari da damar samun bashi mara kuɗin ruwa. Wannan ya bai wa matasa damar kafa sana’o’in dogaro da kansu, wanda hakan ya rage zaman kashe wando da kuma bunƙasa tattalin arziƙin gida.
Salon Jagoranci:
Namadi ya shahara da mutunci, da kula da jama’a kai tsaye. Ya kasance shugaba mai gaskiya da aiki tuƙuru, wanda hakan ya sa ake ganin sa a matsayin jagora abin koyi.
Tasiri Mai Dorewa
A gwamnatinsa ya tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a jihar Jigawa. A yau, jihar Jigawa tana kan tafarki mai kyau na ci gaba, inda Namadi ya gina kyakkyawan yanayi da samar da dama ga matasa da al’ummar jihar baki ɗaya. Wannan lambar yabo ta Gwamnan Shekara tana nuna yadda Namadi ya kasance jagora mai hangen nesa da kyakkyawan shugabanci.