Gwamnan Zamfara Ya Gabatar Ta Liyafar Cin Tuwon Sallah Da Marayu

•Na Zama Ubansu –Matawalle

A lokacin da iyaye ke alfahari da ’ya’yansu, musamman a wajen shugulgulan sallah, abin alfaharin ‘ya’ya ne su ga su na cin abinci tare da iyayensu. Saboda haka ne Gwamnan Jihar Zamfara, Hon. Bello Matawale, ya dauke wa marayun jihar kewa, inda ya shirya gagarumar liyafar cin abincin sallah tare da su da kuma tattaunawa da su na tsawon lokacin a gidansa da ke Gusau, babban birinin jihar Zamfara.

Gwamna Matawale ya bayyana cewa, “wadannan yara ba marayu ba ne, ni ne ubansu. Don haka duk dawainiyarsu zan dauke masu, don ganin sun samu ingantaciyar rayuwa tamkar su na gaban iyayensu.”

Kuma ya dau alwashin ganin sabunta masu dakunan kwana da kuma aurar da wadanda su ka samu mazaje daga cikinsu.

Gwamna Matawale ya yi kira ga al’umma da cewa, “da sun san yadda Allah ke daukaka bawansa da yalwa arzikinsa da gafara gare shi sakamakon taimakon marayu da ba su bar Maya ko daya na gararanba a gari ba.

A kan haka ne ya yi kira ga amsu hannu da shuni da ‘yan kasuwa da mu daure su sadaukar da wani sashe na Abu da suke samu dan taimakon marayu.

A nasa jawabin, Babban Sakatare a Maikatar mata da kananan yara ,Wanda kuma alhakin rikon gidajan marayun ke hannu sa, Alhaji Yusuf Abdullahi Bakura ya bayyana godoyar sa ga Allah ya sanya yau marayu sunzamo masu gata a Zamfara.kuma ya jin jina wa Gwamna Bello Matawale na kin cin liyafar abincin Sallah da iyalinsa sai da marayu.

Alhaji Yusuf Bakura ya  bayyana cewa’ gwamna Matawale ya ba kowane maraya Naira Dobo goma Barka da Sallah .wannan karamcin da mai girama gwamna yayi ubagiji ya sakamasa da herin sa.

Babban sakataren ya kuma bayyana matsalolin da ke cikin gidan marayun da kuma wasu bukatunsu Wanda anan take mai girma gwamnan ya dau alwashin magance su.

Kuma ya bayyana adadin marayun da Gwamna yaci abuncin sallah da su ,su dari ne mazan su da matansu.kuma ya jin jinawa gwamnan duk da aikinsa na farko da ya fara shine ziyartar gidan marayu da kuma mikamasu Rabin albashinsa na kowane wata har zuwa saukarsa mulki.

LEADERSHIP A YAU ta nemi jin ra’ayin manyan da su ka taya Gwamna Matawale cin abinci da marayun.

Alhaji Ahmad Hussaini, Babban Sakataren tsare-tsaren na jam’iyyar PDP na jihar Zamfara ya bayyana cewa, “wannan liyafar da mai daraja gwamna yayi da marayu tunatarwa ce ga mu alumar jihar Zamfara, Kuma kalubale ne ga masu hannu da shuni da ‘yan kasuwar mu rika taimakon marayu. Haka ya kamata shugaba ya zamo wajan fadakar da aluma abunda zai amfane su duniya da lahirar su.”

Hon Asabe Kanoma ita ma ta bayyana jin dadinta da yadda gwamnatin jihar Zamfara ke gabatar da liyafar cin abincin Sallah ga maru a duk shekara.jin jina ga sabon gwamna da yazo da nashi salon da yafi na wadanda suka gabata na sadakatu jariya daga cikin albasgins .ya kamata sauran gwamnoni suyi koyi da gwamna Bello Matawale waja ji kan marayu. Kuma duk alumar da take taimakon marayu Allah ,zai taimaketa kuma ya kare ta daga sharin bala’oi.

Exit mobile version