Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar tsaro na gwamnatin jihar, inda ya kuma yi alkawarin ci gaba da yakar ‘yan bindiga a jihar.Â
A cikin sanarwar da babban mai taimaka masa a fannin yada labarai Sulaiman Bala Idris, ya fitar a jihar a zaman majalisar, gwamna Lawal ya karbi bayanai daga wajen hukumomin tsaro na jihar kan fannin tsaro.
- Yadda Aka Raba Jadawalin Gasar Zakarun Turai
- Kyakkyawar Alakar Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Na Haifar Da Ci Gaba Mai Armashi
Zaman wanda ya gudana a dakin taron na fadar gwamnatin jihar da ke Gusau, babban birinin jihar, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin ‘yan jihar.
Kazalika, gwamna Lawal ya kuma yi kira ga shugabanin hukumomin tsaron jihar, da su kara kaimi wajen tarwata sansanin ‘yan bindiga da ke daukacin fadin jihar.
Bugu da kari, ya umarce su da su tura jami’insu da kuma motocin yaki domin su rinka gudanar da yin aikin sintiri a kan manyan hanyoyin jihar inda kuma ya yi alkawarin goyon bayan gwamnatinsa a gare su da kuma ba su kayan aikin da suke bukata.
Gwamnan ya kuma bayyana wa shugabanin hukumomin tsaron jihar damuwarsa kan ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan jihar, musamman a manyan hanyoyin Gusau zuwa Funtua, Magami zuwa Dangulbi, Dan Kurmi zuwa Anka da kuma Magami zuwa Dansadau.