Khalid Idris Doya" />

Gwamnati Ta Kaddamar Da Zabgai Don Sama Wa Matasa Aikin Yi, In ji Musajo Buba

MUSA BUBA MUHAMMAD Shi ne shugaban hukumar inganta rayuwar mata da matasa na jihar Bauchi wato BASYWORD a takaice, a hirarsaLEADERSHIP A Yau Asabar, ya bayyana dalilansu na daukan matasa masu hidimar tsaro su 1,400 a jihar Bauchin ya kuma yi karin haske sosai kan shirin da suke da shi na inganta rayuwar mata da matasa, haka kuma ya yi fashin baki sosai dangane da ZABGAI da suka diba. KHALID IDRIS DOYAne ya tattauna da shi kamar haka:

Da fari da wa muke tare?

Sunana Musa Buba Muhammad shugabantar hukumar inganta rayuwar mata da matasa na jihar Bauchi wato (BACYWORD) a takaice.

 

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da wasu matasa masu hidimar tsaro na Zabgai, ka yi mana karin bayani kan wannan da kuma dalilinku na kafawa?

Muna godiya wa Allah da ya ba mu ikon daukan wadannan ma’aikatan a karkashin jagorancin gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar, a bisa la’akari da halin da jama’a suke ciki na rashin aikin yi, musamman a wajen matasanmu. wannan dalilin ne ya sanya mai girma gwamnan jihar Bauchi ya yi hangen nesa ya duba cewar ta yaya ne za a yi kokarin rage wannan radadin rashin aikin da ke cikin al’umma, a bisa wannan tunanin ne ya sanya aka kirkiro da wannan aikin na ‘ZABGAI Security’.

Na farko dai ita Zabgai kamfani ce na tsoffin sojoji, wadanda su sun kwarance wajen harkar tsaro kuma suna da satifiket dinsu mai rijista a kasa gaba daya; a bisa ganin haka, da wannan kwarewar tasu sai muka amince da su. ka san idan ka dauki yaro ka ce ka koya masa gadi idan bai san yadda zan yi ya fara gadin ba sai ka ga an yi wani abun na daban. don haka ne yanzu a karin farko mun dauki matasa 1,400 a cikin kananan hukumomi 20 da muke da su a fadin jihar nan ta Bauchi. wadannan matasa 1,400  sai muka damkasu ga Zabgai domin su basu horaswa kan harkar tsaro, kamfanin ta kuma basu horon na tsawon sati uku wanda suka yi a sansanin horon ‘yan yiwa kasa hidima da ke Wailo, bayan sun kammala mun gamsu da irin horon da suka samu, domin a lokacin faretin sallamarsu da fitarsu matasan nan sun nuna mana cewar abun da gwamnati ta turasu su koya sun tsaya sun koya domin mun gamsu da abubuwan da suka nuna a wajen faretin yayensu, sannan kuma an koyar da su da kyau. Saboda haka ne yanzu wadannan matasa 1,400 suna karkashin wannan kamfani mai suna ‘Zabgai Security Serbices Limited’. Bayan wadannan matasa 1,400 akwai kuma wasu matasan 600, kila ma za ku fi mu sani domin kuna bangaren labarai ne, akwai takaddamar da ake yi a tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da kamfanin (Spider Webs) wanda a gwamnatin da ta gabata suka yi shigen irin wannan tsarin namu, to da aka zo sai gwamnati ta ce ta amince musu su Spider Webs su dauki matasa 600 daga wajensu, idan ka hada dukka an samu matasa 2,000 kenan, wadannan matasan sune gwamnati ta bayar da izinin a daukesu, kuma an daukesu aiki wanda gwamnatin jihar Bauchi ce za take biyansu albashi duk wata.

 

Takamaimai mene ne hikimar da ke cikin kafa wannan matasa masu hidimar tsaron?

Hikimar da ke cikin hakan abu biyu ne, na farko mu dan yaki rashin aiki da fatara da ke addabar al’ummarmu a yau, ka ga an samar wa matasa dubu biyu aikin yi, wadanda kowani matashi a bisa tsarin da aka yi kowanne a cikinsu zai karbi albashin naira 15,000 ne a kowace wata, sannan kuma a cikinsu din albashinsu ya kasu kashi uku ne, a cikin wannan bangaren masu daukan albashin dubu goma sha biyar akwai kuma masu bin diddiginsu ‘superbisors’ da za biyasu dubu 18,000 a kowace wata, sannan kuma akwai shuwagabaninsu su kuma za su dauki dubu 25,000, wannan shi ne albashin da aka tsara musu kowace wata. Na biyu kuma, alfanun dibansu a cikin al’umma, abun da ya sanya gwamnati ta yi tunanin a dibi wannan din, shine kasantuwar halin da al’ummanmu suke ciki a yau, kanana-kananan sace-sace sun yi yawa, tabarbarewar tarbiyya a cikin al’umma, ka ga sai muka duba mu ka ga cewa kila aiyukan dan sanda ba zai iyu su iya shiga koina da ina ba; don haka ne muka dauki wadannan matasa domin su taimaka wajen samar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a, wadannan sune hujjarmu na daukan wannan matasa masu hidimar tsaro a wannan lokacin.

 

To meye sanya idan damuwarku ci gaban tsaro da samar da aiyukan yi ne ba ku ci gaba da tafiyar da matasan da tsohowar gwamnati ta dauka na Spider sai kuma kuka zo kuka kirkiro naku maimakon ku ci gaba da kula da su don samar da aiyukan yi?  

Idan ka zo aiki wajen da aka tura ka, sai aka baka gida ko na haya ko kuma ka saya, watakila za ka dan yi kwaskwarima wa gidan kafin ka shiga ko? Wata kila ma ka ce wannan gidan ma bai yi maka ba, a sake nemo maka wani don ka shiga, iri daya ne da wannan tsarin, wancan gwamnatin da ta kawo tsarin Spider Webs akwai wasu tsarukan da mu bamu yarda da su a ciki ba. yanzu zan baka misali, yanzu haka maganar da na ke yi da kai na rubuta takarda wa Spider Webs na ce musu su turo mana jerin sunayen mutane 600 da aka umurcesu su dauka, da cewa a ina suke a kawo mana su. Meye sa na ce babu tsari? ‘yan Sifaida sun yi kungiyarsu sun zo nan wajen wadanda suke takaddama da gwamnati kan cewar ba a bisaya su kudinsu ba, suna bin gwamnati kudi, na ce musu a’a ku yi hakuri baku bin gwamnati kudi, kasan meye sa na ce maka basu bin gwamnati kudi? Su kamfaninsu ce ta daukesu aikin ba gwamnati ba. kaman kai ne za ka yi gidinin gida ga Injiniya sai ka ce wa Injiniya a nawa za a yi min ginin gidana har a kai ga karshe, ya ce maka miliyan biyu, idan ka dauki miliyan biyu ka ba shi meye laifinka da kafinta? Meye laifinka da mesin? Babu ruwanka da su, kai dai naka a gama gida a baka makulli ka je ka shiga, to ka ga tun da fari ba a fada musu gaskiya ba don ba a bi kundin tsarin da ta dace ba, su kamfani ne suka daukesu, su kuma gwamnati ce ta ke biyansu.

 

Amma sun yi yarjejeniyar wa’adi?

Shi duk abubuwan da ba a yi din ba, ka ga mu namu tsarin na Zabgai mun yi yarjejeniyar wata 12 ne, kuma mun yi hakan a rubuce na wata goma sha biyu ga kuma kudin da za mu biya ku sun kuma yarda. Wata sha biyu idan ya yi, ka ga idan muka ga akwai dama sai mu sake sabunta yarjejeniyarmu, idan ya kare sai mu ce musu daman iyaka yarjejeniyarmu da ku kenan. ga su babu irin wannan tsarin a Spider Webs. Don ma wai kar a barsu su tafi haka nan muka ce su kawo mutane 600 a cikinsu. Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

 

Exit mobile version