Gwamnati Ta Waiwayi Malaman Makaranta Da Likitoci Yayin Da…

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

 

 

A ranar Laraba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da kudirin sashen zartarwa ga Majalisar Dattawa don neman a kara yawan shekarun ritaya ga malaman makaranta a kasar nan daga shekaru 60 zuwa 65.

Kudirin ya kuma nemi tsawaita shekarun aikin malanta daga shekaru 35 zuwa 40.

A cikin wasikar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, kuma ya karanta a farfajiyar majalisar, Buhari ya bayyana cewa dokar za ta samar da daidaiton shekarun ritaya ga malamai a Nijeriya.

Ya ce matakin da aka dauka na kara shekarun ritaya da kuma shekarun yin aiki ya yi daidai ne da Sashe na 58 (2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Wasikar ta ce, “Muna nema a aiwatar da daidaita shekarun ritaya ga malamai a Nijeriya bisa kudurin doka na 2021 da muka aika wa majalisar kasa don dubawa.

“Wannan ya kasance ne a sashi na 58, karamin sashi na 2 na Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara), na tura gabanku don daidaita shekarun ritaya ga malamai a Nijeriya bisa kudirin doka na 2021, don Majalisar Dattawa ta yi la’akari da su.

“A dokar ta 2021 a Nijeriya ana neman a kara shekarun ritaya ga malamai daga shekaru 60 zuwa 65, sannan kuma a kara shekarun da za a iya yin aikin malanta daga 35 zuwa 40.” Kamar yadda wasikar ta ruwaito.

Exit mobile version