Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta ɗauki matakin ladabtarwa kan manyan makarantun da suka gaza gabatar da jerin sunayen ɗalibai bayan kammala ɗaukan sabbi.
Wannan umarni ya fito ne a cikin wata takarda daga hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) mai taken bayani kan bayar da adadin ɗalibai da aka amince da su tun daga 2017 zuwa yanzu, wanda mai ba da shawara kan harkokin sadarwa na JAMB, Fabian Benjamin, ya fitar.
Wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin hana maguɗi da damfara wajen samun takardun digiri a Najeriya. An umarci makarantu su miƙa sunayen waɗanda suka kammala rajista ga ma’aikatar ilimi ta tarayya cikin watanni uku bayan rajista, ta hanyar tsarin CAPS na JAMB.
JAMB ta jaddada cewa ba za a yarda da duk wata shiga makaranta ɗaukar dalibai da aka boye ba, kuma makarantun da suka kasa bin wannan ka’ida za su fuskanci hukunci mai tsauri.
Wannan umarni ya biyo bayan kafa kwamitin bincike na ministoci kan maguɗi wajen samar da takardun digirin bogi, wanda aka ƙirƙiro domin magance matsalar sayar da takardun digiri na jabu, musamman daga Jamhuriyar Benin. Ma’aikatar ilimi ta umarci JAMB da ta tabbatar da cikakken bin dokar tsarin CAPS tare da tabbatar da makarantu sun gabatar da sunayen ɗalibai a kan lokaci.