Gwamnatin jihar Bauchi ta sauke shugaban makarantar Sakandarin Gwamnati ta jeka-ka-dawo (GDSS) da ke Kirfi, Malam A (an sakaye suna), daga muƙaminsa bayan an same shi da laifin Amin gaba da kayan makaranta. Hakanan, an sauke babban jami’in makarantar, Malam B (an sakaye suna), wanda ya haɗa baki da shi wajen sayar da kayan gwamnati.
Rahoton kwamitin bincike na hukumar kula da malamai ya bayyana cewa jami’an makarantar sun sayar da gadajen dalibai 32, tukwane 9, da kuma falangen rufin kwano na zinc masu yawa. Wannan laifi ya sabawa doka da ka’idojin aikin gwamnati.
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
- Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Kwaskwarimar Majalisar Dokoki Kan Naira Biliyan 7
A matsayin hukunci, hukumar ta rage musu muƙami da matakin albashi guda, tare da sauya musu wurin aiki zuwa wasu makarantu daban-daban, inda za su ci gaba da koyarwa a matsayin malamai na yau da kullum ba tare da wani matsayi na shugabanci ba.
Hakanan, an umarce su da su dawo da adadin N597,000, da aka ƙiyasta darajar kayan da suka sayar, tare da ƙarin N72,000 da tsohon shugaban makarantar ke binsa a matsayin alawus na masu gadi.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin gano kayayyakin da aka sace da kuma tabbatar da bin doka da oda a dukkan makarantun gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp