Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya amince da Naira 104,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan gwamnati, wanda ya zamo shi ne mafi yawan albashi a Jihohin Nijeriya.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a daren Talata a lokacin da yake ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a gidan gwamnatin jihar da ke Owerri.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 8 A Kaduna, Sun Jikkata Wasu
- PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro
Rahoton Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ya ce, Uzodimma ya bayyana cewa ƙarin albashin na nuna yadda gwamnatinsa ke kula da jin daɗin ma’aikata da bunƙasar tattalin arziƙi.
Albashin ya tashi daga Naira 76,000 zuwa Naira 104,000.
Haka kuma, albashin likitoci ya ƙaru daga Naira 215,000 zuwa Naira 503,000, sannan malaman jami’a da manyan makarantu za su riƙa samun Naira 222,000 maimakon Naira 119,000.
Uzodimma ya ce ƙarin albashi zai inganta rayuwar ma’aikata, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru daga Naira miliyan zuwa sama da Naira biliyan uku a kowane wata, yayin da bashin jihar ya ragu daga sama da Naira biliyan 280 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 100.
Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin mai, yana cewa duk da ya jawo tsadar rayuwa, amma ya ƙara yawan kuɗin da ake raba wa jihohi kuma ya bai wa gwamnati damar yin sauye-sauye.
Gwamnan ya ƙara da cewa daga ranar 27 ga watan Agusta, gwamnati za ta fara biyan kashin ƙarshe na kuɗaɗen fansho da ake bai wa tsoffin ma’aikata, wanda jimillarsa ya kai Naira biliyan 16.
A nasa martanin, shugaban Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) a Jihar Imo, Uchechigemezu Nwigwe, ya ce sabon albashin babban nasara ne ga dukkanin ma’aikata a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnan ya ceci ma’aikata daga matsin tattalin arziƙi, kuma ya sanya Imo cikin jihohin da ke da albashi mafi tsoka a Nijeriya.
Nwigwe ya yi alƙawarin cewa ma’aikata za su saka wannan alheri ta hanyar yin aiki da ƙwazo da inganci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp