Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da mataki na uku na biyan kuɗaɗen fansho, inda ya raba Naira biliyan biyar ga ma’aikatan fansho.
Wannan ya kawo jimillar kuɗaɗen da gwamnatinsa ta biya zuwa Naira biliyan 16 tun bayan hawansa mulki.
- Everton Ta Sallami Kocinta, Sean Dyche
- Jami’an Tsaro Sun Kawar Da Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Baƙo-baƙo Da Mayaƙansa A Katsina
A cewar mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wannan biyan wani yunƙuri ne na tallafa wa tsoffin ma’aikatan da suka yi wa jihar hidima na tsawon shekaru.
A baya, gwamnatin ta biya Naira biliyan shida ga ma’aikatan fansho masu ƙasa da matakin aiki na 10, sannan ta biya Naira biliyan biyar ga waɗanda suka yi aiki na tsawon shekaru 35.
Gwamna Abba, ya sake jaddada ƙudirinsa na biyan dukkanin kuɗaɗen fansho da alawus-alawus da ake bin gwamnatin, tare da alƙawarin cewa duk tsoffin ma’aikata za su samu haƙƙoƙinsu ba tare da jinkiri ba.
Ya ce, “Wannan gwamnati ta ƙuduri aniyar magance dukkanin matsalolin da tsoffin ma’aikata ke fuskanta.
“Za mu ci gaba da fifita walwalarsu da tabbatar da cewa dukkanin haƙƙoƙinsu an biya cikin ƙanƙanin lokaci.”
Mataki na uku na wannan biyan fansho alama ce ta jajircewar Gwamnan wajen dawo da martabar tsarin fansho na Jihar Kano da kuma inganta rayuwar tsoffin ma’aikatan gwamnati.