Gwamnatin Jihar Kano ta rufe asibitin kuɗi guda 35 cikin watanni 12 da suka gabata saboda karya dokokin gudanar da ayyukan lafiya.
Muƙaddashiyar Daraktar Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano, Khadijah Sa’id, ta ce an hukunta cibiyoyin lafiya sama da 100 bisa laifuka daban-daban.
Ta ce daga cikin laifukan da aka gano akwai gudanar da aiki ba tare da lasisi ba, rashin sabunta rajista da kuma ɗaukar ma’aikatan lafiya waɗanda ba su da ƙwarewa.
Ta bayyana cewa an rufe wasu cibiyoyin na ɗan lokaci domin su gyara kura-kuransu, yayin da za a iya soke rajistar waɗanda suka aikata manyan laifuka.
Ta buƙaci masu cibiyoyin lafiya masu zaman kansu su mallaki lasisin aiki mai inganci, su riƙa sabunta rajistarsu a kan lokaci, tare da tabbatar da cewa ƙwararrun ma’aikatan lafiya ne kawai ke kula da marasa lafiya.














