Shirin Jihar Kano na bunkasa noma da kiwo (KSADP), ya jaddada aniyarsa na yi wa akalla shanu miliyan daya da tumaki da akuyoyi dubu 800,000 rigakafi, a shirin rigakafin dabbobi na sheka-shekara da aka saba yi Jihar Kano.
Bankin Musulunci na duniya tare da Cibiyar ‘Libes and Libelihood Funds’ ne za su dauki nauyin shirin kamar yadda suka saba, inda ake sa ran kashe kimanin naira miliyan 160, domin sake bunkasa lafiyar dabbobin tare da kyautata wa makiyaya.
- Gajiya Ce Ta Sa Na Fadi Yayin Tantance Ni A Majalisa — Balarabe
- Akwai Yiwuwar Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa Dubu 100 Ko 200 – NLC
A sanarwar da mai magana da yawun cibiyar (KSADP) ya fitar, Ameen K. Yassar, wanda aka raba wa ‘yan jaridu, shugaban kula da shirin na Jihar Kano, Malam Ibrahim Garba Muhammad, ne ya bayyana hakan a lokacin bude taron wayar da kan al’umma, musamman makiyaya a kan shirin, wanda aka kaddamar a Fadar Hakimin Kura da ke Karamar Hukumar ta Kura a Jihar Kano.
“Babu shakka, wannan shiri ya kudiri sake kyautata kula rigakafin dabbobi, domin kuwa lafiyar dabbobinku na da kyakkyawar alaka da taku lafiyar tare da habbaka tattalin arzikinmu baki-daya,” in ji Shugaban.
“Babban muhimmin abin da ya hada mu a nan shi ne, sake wayar muku da kai a kan wannan rigakafi ta dabbobi tare da neman hadin guiwar dukkanin shugabanninku, domin ganin wannan shiri ya cimma nasara,” kamar yadda ya bayyana.
Har ila yau, shirin rigakafin na shekara-shekara, ya kunshi wasu shirye-shirye da dama da suka hada da kyautata tare da bunkasa Cibiyar Kadawa ta kyankyasa, gina cibiyar tattara madarar shanu, bunkasa kasuwar dabbobi da sauran makamantansu tare da kyautata rayuwar makiyaya baki-daya.
”Muna sa ran a nan kusa in sha Allahu za mu bayar da aikin katange iyakokin dabbobi a Kano, wanda ko shakka babu hakan zai kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a wannan jiha tamu ta Kano”, a cewar tasa.
Hakimin Kura, Dokajin Rano, wanda Alhaji Balarabe Muhammad ya wakilta ya bayyana cewa, daga tsawon shekaru uku zuwa yanzu, ba a samu wani rahoto na bullar wata cuta ko annoba da ta afka wa dabbobinmu ba, sakamakon wannan rigakafi da Cibiyar KSADP ke bai wa dabbobin namu duk shekara.
Haka zalika, ya umarci Dakatai da sauran shugabannin makiyaya da ke zaune a wadannan yankuna, da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin rungumar a wannan rigakafi da za a aiwatar a wannan shekara duba da irin muhimmancin da yake da shi.
A nasa tsokacin, a maimakon al’ummar Karamar Hukumar Kura, Malam Zubairu Muhammad cewa ya yi, tuni sun saba da wannan rigakafi, domin kuwa tuni sun ga amfaninta tsawon shekaru uku, saboda haka suna sake bayar da tabbacin bayar da dukkanin hadin kai wajen gudanar da shirin.
“Tuni mun ga amfanin wannan rigakafi da aka gudanar tun a baya, don haka muna godiya ga Bankin Musulunci na duniya tare da Cibiyar ‘Libes and Libelihood Funds’, da rashin gajiyawarsu wajen ci gaba da dawainiya da wannan shiri”.
Shi ma a nasa jawabin, Daraktan Sashen kula da dabbobi na yankin Rano, Dakta Idris Ibrahim ya yi jan hankali a kan muhimmancin wannan rigakafi, inda ya bayar da shawarar cewa, ya kyautu a sanya karnuka cikin wannan rigakafi, tun da dai makiyayan na ta’ammali da su yayin kiwon nasu.