Gwamnatin Jihar Katsina za ta sake samun kudin bankin duniya a karkashin shirin nan na inganta ilimi mai suna “BESDA”, domin gudanar da ayyukan ilimi.
Shugaban hukumar ba da ilimin bai-daya na Jihar Katsina, Lawal Buhari Daura ya bayyana hakan a lokacin yake bude taron bunkasa kwazon aiki na kwana 3 domin amfani ga jami’an tattara bayanai da kididdiga na ma’aikatar ilimi.
- Alkawurana Ga ‘Yan Nijeriya Kan Tsaro, Zaman Kashe Wando Da Tattalin Arziki — Kwankwaso
- Ma’aikatan N-Power Sun Yi Zanga-Zangar Kin Biyansu Hakkokinsu A Bauchi
Bankin duniya ne karkashin shirin BESDA hadin gwiwa da hukumar ba da ilimin bai daya suka shirya ba da horon a Kano.
Ya ce biyo bayan rahotannin da hukumar tantancewa ta mika ma BESDA, yanzu Jihar Katsina ta cancanci kara samun kudin na bankin duniya domin gudanar da ayyukan BESDA a jihar.
Shugaban hukumar ya ce za a maida hankali wajen amfani da kudaden ga ayyukan da za su kusantar da mutane ga makarantu.
Ya bukaci wadanda suka halarci horon su maida hankali don ganin sun yi amfani da abin da suka koya a wuraren ayyukansu daban-daban.
Tun da farko, Daraktan sashen tsara bincike da kididdiga na hukumar SUBEB, Lawal Kofar Sauri ya bayyana cewa jami’an da ake ba horon guda 73, an zabo su ne daga kananan hukumomin Jihar Katsina 34 hadi da hukumar SUBEB.
Ya yi nuni da cewa shirin BESDA ya samar da kwamfutocin tafi-da-gidanka, hadi da manyan wayoyon hannu ga jami’an da ke aikin tattara bayanai da kididdiga na hukumar ilimin domin tattara bayanai masu sahihanci da za a yi amfani da su.