Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da sace mutane 13 bayan wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai ƙauyen Ayetoro Kiri da ke Karamar Hukumar Kabba/Bunu.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce mafarauta sun kashe ’yan bindiga huɗu yayin musayar wuta, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
- Wakilin Sin Ya Sake Gargadin Japan Da Ta Janye Kalamanta Na Kuskure
- Tarayyar Turai Ta Ɗauki Nauyin Shirin Zaman Lafiya Na Yuro Miliyan 5.1 A Zamfara
Fanwo, ya bayyana cewa hare-haren da ke faruwa a jihohin Nija da Kwara da ke maƙwabtaka da Kogi ne suka tilasta wa masu laifi shigowa cikin jihar.
Ya ce yankin da aka kai harin na manoma ne kuma yana buƙatar ƙarin tsaro.
Ya ƙara da cewa an tura sojoji, ’yansanda, da sauran jami’an tsaro zuwa yankin.
Gwamnatin jihar ta ce ana ci gaba da farautar ’yan bindigar a cikin daji domin ceto mutanen da suka sace, tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa an shawo kan lamarin.














