Gwamnatin Jihar Sakkwato ta aminta da kashe tsabar kudi Naira Biliyan 20.3 domin sayen abincin da za a tallafawa al’umma domin rage radadin cire tallafin man fetur da kuma gudanar da wasu ayyuka.
Kwamishinan harkokin Adddini, Jabir Sani Mai- Hula ne ya bayyana hakan bayan kammala taron farko na Majalisar Zartaswar Jihar a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu, inda ya ce, gwamnatin ta kafa dokar daukin gaggawa kan samar da abinci.
“Majalisar Zartaswar Jiha ta aminta da sayen buhu 57, 000 na shinkafa mai nauyin kilo 50 a kan Naira Biliyan 2.5 da buhu 26, 000 na Gero mai nauyin kilo 100 a kan Naira Biliyan 1.4 wadanda kudinsu suka kama Naira Biliyan 3.9.
“Za a raba su ne a fadin jihar, domin tallafawa al’umma kan radadin janye tallafin man fetur a bisa ga matsin tattalin arziki da ake ciki.” Inji Mai-hula
Kwamishinan ya kara da cewa, Gwamnatin jiha da hadin guiwar Gwamnarin Tarayya sun kuma aminta da saye da raba buhun Masara 44, 000.
Ya ce gwamnatin jiha ta bayar da damar sayen motoci 50 kirar Toyota masu daukar mutane 18 da Toyota Camry 20 domin jigilar matafiya a kan kudi naira biliyan 3.4. Ya ce za a yi amfani da motocin a tafiye- tafiyen jihohi da cikin jiha, a yayin da za a yi amfani da motocin Camry wajen jigilar mata zalla a cikin jiha.
Haka ma Majalisar ta ce a bisa ga kokarin gwamnati na magance matsalolin tsaro ta aminta da sayen motoci kirar Toyota Hilux 66 a kan naira biliyan 2.6 wadanda za a rabawa ofisoshin ‘Yansanda a Kananan Hukumomi 23 a yayin da sauran za a rabawa sauran jami’an tsaro.
Kazalika, Majalisar ta aminta da gina gidaje 500 a kan naira biliyan 7.4 a Kalambaina. Za a gina gidaje 300 masu dakuna 3 da kuma 200 masu dakuna 200 a yayin da za a kashe naira biliyan 1.8 domin shimfidawa da gyaran hanyoyi.