Gwamnatin Tarayya Na Ayyukan Tituna 524 A Fadin Kasar Nan -Fashola

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya tabbatar da cewa; ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya tana gudanar da ayyukan tituna 524 a wurare daban-daban na yankuna shida na kasarnan.

Fashola ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a Abuja ga wakilan Kwamitin majalisar wakilai wanda dan majalisa Ahmed Birchi ke jagoranta.

Fashola ya tabbatar da cewa; suna aikin gina titunan ne domin bunkasa bangaren tattalin arziki da kuma saukaka wa masu gudanar da kasuwanci domin su samu hanyoyin da za su rika gudanar da kasuwancin na su.

Exit mobile version